Sana’ar Dinka Zanin Gado

Dinka

Zanin gado yadi ne wanda ake shimfidawa a kan gado don rufe katifa da kuma kawata gadon da aka shimfida.

Yanzu zanin gado ya canja salo domin ana kawata su fiye da da wajen yin amfani da yaduka na alfarma dama kananun matasai wanda aka fi sani da throw pillows, yana kawata gado matuka musamman idan aka yi amfani da kaloli da suffa kala-kala.

Sana’ar na da matukar riba sosai saboda kowane gida na amfani da zanin gado kuma musamman na zamani wanda ke matukar kawata shimfida.

Abubuwan dubawa idan za ai dinkin zanin gado shi ne girman gadon da za’a yi wa wannan zanin gadon, gadaje kala-kala ne akwai 6/7 akwai 6/6 da sauran su.

Mai yin wannan sana’a zai dinka zanin gado daban- daban ma’ana na girman gadaje daban-daban da kuma irin kansa shi zanin gadon da za a yi, wannan ya sa zannuwan gado duke kala-kala kama daga ‘simple bed spread’ wato zanin gado mai sauki wanda bai da tarkace a jiki da mai tattara da mai soso da dai saurance.za.

Ki iya dinkawa da kanki za kuma ki iya siya a kasuwa ki sayar.

Abubuwan da ake bukata yayin dinka zanin gado

Keken dinki

Yadin dinka zanin gado, Almakashi, Fibre ko soso

Kujeran zama,

Yadda ake amfani da su.

1.Keken dinki: Ana amfani da shi ne wajen dinka zanin gado mai dinki za ta auna yadi ne dangane da irin girman gadon da take son dinkawa zanin gadon. Misali zanin gado irin Wanda aka fi amfani da shi a kan gado shi ne 6/7shi ana amfani ne da yadi 4 yadi 3 za ki kalmashe gefe gefen zanin gadon da kika yanka da keke da zare kalan yadin da kika yanka yadi da yadda kika ajiye gefe, sai ki auna shi daidai na dinka pillow sai ki yanka ki ninke shi ki dinka shi. Akwai zanin gado half set da kuma full set wato wanda suke da matasai da yawa da kuma aoao ko fiber

  1. Yadin dinka zanin gado akwai yaduka kala kala Wanda ake dinka zanin gado dashi akwai London bedsheet akwai american bedsheet.

Mai wannan Sana’a idan za ta dinka zanin gadon ya kamata ta yi amfani da yadi mai kyau wanda zai dade ta na amfani da shi kuma ba zai yi saurin tashi ba. American bedaheet kenan, mai dinka zanin gado za ta samu yadin a kasuwa

  1. Almakashi: Almakashi dai ana amfani da shi ne bayan an gama dinka zanin gadon da kuma wurin raba yaduka wato raba yadin zanin gado da pillow
  2. Fibre ko soso-soso ne wanda ake amfani da shi gun dinka kananan pillow don kawata gado da shi kuma ana amfani da shi don yin sweet ko throw pillow.

Fibre ya fi soso dadewa bai saurin bacewa kuma ya fi tsada.

  1. Kujera: Ana amfani ita ne wajen zama don taka keken dinki da za’a dinka zanin gado.
  2. Leda: Leda ana amfani ita ne idan an gama dinka zanin gado da kuma pillow sai a goge da dutsen guga a saka cikin Leda a rika i sayarwa

 

 

Exit mobile version