Sana’ar Kwalliya Da Adon Mata Na Kawo Alheri Ga Mata – Amina

Daga Muazu Hardawa, Bauch

Wata mai sana’ar yin kwalliya da samar da kayan abinci don bukukuwa Malama Amina Musa Jibrin ta bayyana sana’ar a matsayin sana’a mai samar da rufin asiri ga mata a cikin gidajen su tare kuma da shawartar iyaye mata kan su lura da iyalan su ta hanyar samun sana’a a cikin gida da za ta riƙa samar musu kuɗin biyan bukatun su na yau da kullum.

Amina Musa Jibrin ta bayyana haka ne lokacin da ta shirya bukin baje kayan amfanin gida na kwalliya da na abinci da kuma kayan yiwa mata kwalliya na inganta jiki da muhalli, don haka ne ta shirya don wayar da kan mata, inda mata da dama suka baje kayan da suke sarrafawa na sana’a a cikin gida wanda aka yi a cibiyar ‘yan jaridu da ke Bauchi.

Saboda haka ta ja hankalin mata kan su zauna a gidajen mazajen su amma su tabbatar sun samu abin yi don lura da kan su da yaran su domin yanzu lokaci ne da ba za a dogara da komai sai miji ya yi wa mata a cikin gida ba, ya  kamata itama ta taimaka wajen samun hanyar dogaro da kai.

Don haka ta ce tun tana Jami’ar ATBU, ta riƙe sana’ar yin kek da adon gida da kwalliyar wurin taro da sauran ayyukan ci gaba da mata ke yi.

Inda ta ce haƙiƙa wannan sana’a ta rufa mata asiri har ta gama jami’a kuma yanzu shekaru biyar kenan tana wannan sana’a. Don haka ta bayyana cewa ta samu alheri kan sana’ar har zuwa wannan lokaci da a halin yanzu take koyar da mata da maza yadda za su amfana da wannan sana’a domin su samu dogara da kan su.

Don haka Amina Musa Jibrin ta bayyana cewa wannan buki ta shirya shi ne, kuma ta gayyaci waɗanda suka ƙware wajen yin kayan abinci da kek da fashin gugguru da gwanayen yin lalle da ɗaura kallabin mata da yin adon gida ko wajen taro da kuma masu sayar da kayan kwalliya da sauran masu sana’a irin ta gida da kayan amfanin yau da kullum. Don haka ta buƙaci mazaje su temaki matan su ta hanyar yadda za su riƙa yin kayan amfanin gida domin su dogara da kan su, hakan zai temaka wajen inganta zaman iyali da temakon yara ko da megida ya gaza ta hanyar samun abin hannu.

Haka kuma ta shawarci mata da su kasance masu neman abin kan su kuma su nisanci kashe zukatan su da zama ba tare da neman hanyar dogaro da kai ba, inda Malama Amina ta ƙara da cewa dukkan matar da ta tsaya kan ƙafar ta wajen neman abin kanta ba za ta riƙa kasancewa cikin talauci ko kaskanci ba. Hakan zai taimaka wajen ganin ta samu lura da kanta da iyalanta ko da mijinta bai samu halin yi mata abin da ta ke so ba ta hanyar wadata gida da kayan buƙatu na iyali. Hakan shine zai sa iyalai su dogara da kansu ta hanyar temakon junan su.

Exit mobile version