CRI Hausa" />

Sanarwar Kakakin Watsa Labaru Na Ofishin Jakadancin Kasar Sin Dake Najeriya

A ranar 10 ga wata, jakadan kasar Sin dake Najeriya Zhou Pingjian ya gana da shugaban majalisar wakilan kasar Najeriya bisa gayyatar da aka yi masa, inda ya kalli bidiyon da aka dauka a cikin wayar salula, game da wai “an nuna rashin daidaito kan jama’ar Najeriya a birnin Guangzhou na kasar Sin”, bayan haka kuma ya tabbatar da cewa, a cikin bidiyon, ayyukan da masu aikin dalike cutar COVID-19 na bangaren Sin suka aikata sun dace. Gwamnatin kasar Sin tana daukar dukkan mutanen kasashen ketare dake nan kasar Sin a matsayin daidai wa daida, kuma tana adawa da kowane irin mataki na nuna rashin daidaito, balle ma maganganu da ayyukan nuna bambanci. Ayyukan kandagarki da shawo kan cutar na bukatar fahimta da goyon baya da kuma hadin kai daga jama’ar kasar Sin da ma jama’ar kasashen ketare dake nan kasar Sin, ya kamata bakin dake kasar Sin su bi ka’idojin dakile cutar. Ana sada zumunci a tsakanin kasashen Sin da Najeriya, ofishin jakadancin Sin dake Najeriya na son mu’amala tare da bangaren Najeriya a wannan fannin. (Mai Fassarawa: Bilkisu Xin)

Exit mobile version