Ibrahim Muhammad" />

Sanata Agege Ya Nuna Damuwa Kan Yawaitar Shan kwayoyi Tsakanin Matasa

Sanata Agege

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Omo Agege ya ce, majalisar Dattawa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganim an kara yawan kason kudaden gudanarwa na hukumar Yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ‘NDLEA, domin samar da yanayi na gudanar da aikinsu cikin nasara na dakile tu’ammali da kwayoyi.

Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Babban Mataimaki ga Mataimakin Sshugaban Dattawan. Musa Mujahid Zaitawa ya raba wa manema labarai.
Sanata Omo Agege ya koka da yanda a ke samun yawaitar masu ta’ammali da miyagun kwayoyi musamman a tsakanin matasa wanda a ke ganin sune manyan gobe.
Mataimakin Shugaban Majalisar na fadin wannan ne a lokacin da ya ke ganawa da kungiyoyin Matasa da Talakawa ta kasa da kungiya da ke rajin yaki da safara da shan miyagun kwayoyi da cin zarafin mata su ka ziyarce shi don mika masa bukatu da zai taimaka wajen yaki da shan kwayoyi da kuma karrama shi.
Ya kara da nuna damuwa kan yawaita shan kwaya tare da kira ga Gwamnati akan daukar kwararan matakai da zai kawo karshen wannan mummunar lamari. A bangarensu na majalisar Dattawa za su yi kokari an kara kasafin kudaden da a ke baiwa NDLEA da kuma sakar musu akan lokaci duba da ganin akwai rashin wadatar a kasafin nasu.
Ya ce, duba da irin muhimmancin rawar da NDLEA ke takawa za su duba yiwuwar a sama musu kudade cikin gaggawa kamar yadda a ke samarwa hukumar sauran hukumoni.
Sanata Ome Agege ya ce, matakin da Majalisar Dattawa ta 9 ta dauka shi ne na gudanar da kasafin kudi farkon shekara da duba shi daidai da yanda za a zartar da shi a cikin shekara ba tare da tsaiko ba.
Mataimakin shugaban majalisar Dattawan, Omo Agege ya ce, jahar Kano za ta sami karin gidajen gyaran tarbiyya sakamakon tana daga jihohin da su ke da yawan masu ta’ammali da kwayoyi.
Ya tabbatar wa da ‘yan kungiyoyin cewa za su sami goyon bayan majalisun kasa don maganta lamarin tare da cewa yawaita wayar da kai a cikin al’umma daga masu ruwa da tsaki a cikin al’umma da kungiyoyi da wuraren ibada zai taimaka gaya wajen kauda shan kwayoyi da safararsu.
Omo Agege ya jinjina wa kungiyoyin da kawo wannan sako na jan hankalin majalisa duk kuwa da ba sune farko da ke zuwa majalisar ba amma sune su ka zo da kudurin a duba matsalar NDLEA da basu kwarin gwiwa akan aikinda su ke na hana fatauci da shan kwayoyi.
A nata jawabin tun farko a madadin kungiyoyin Ambasada Mariam Hasan ta koka da rashin kudade wadatattu na gudanarwa ga Hukumar Yaki da sha da fataucin kwayoyin ke fuskanta da neman majalisar Dattawan cikin ikonta ta sahale a kara musu a kuma musu akan lokaci
Sun kuma damu da yawan matasa da a ke samu a ta’ammali da kwayoyi da hakan ke jawo aikata miykgun laifuka.
A yayin ziyarar kungiyoyin sun mika shaidar karramawa ga mataimakin shugaban majalisar Dattawan Sanata Omo Agege bisa yaba ma sa da irin rawarsa ya ke takawa, domin warware matsalolin kasa a majalisar Dattawan.

Exit mobile version