Sanata Al-Makura Ya Cancanci Rike Kujerar Shugabancin APC, Inji Gwamna Sule

APC

Daga Zubairu M Lawal,

A yayin da uwar jam’iyyar APC mai mulki take kokarin gudanar da zaben Shugabannin Jam’iyyar ta kasa yan takara da magoya bayansu kowa na kokari shiga lungu sako domin gudanar da yakin niman zabe.

Gwamnan jihar Nasarawa Injinya Abdullah Sule tuni ya nunawa Duniya goyon bayan Sanata Umar Tanko Al-makura ba wai saboda sun fito daga jihar daya ba sai dan cancanta da ganin Sanata Al-makura a matsayin Gwarzon da zai iya maido da daraja da kimmar jam’iyyar APC a lokaci kankani ga al’umman Nijeriya.

Gwamnan wanda ya yabawa siyasan Sanata Al-makura na hadin kan al’umman daga sasa dabam dabam na jihar yana ganin Sanata Al-makura zai hada kan ya’yan jam’iyyar APC daga ko ina cikin fadin kasan nan ta yadda za a gudu tare a kuma tsira tare.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa ba wai yana tuntubar masu ruwa da tsaki bane kawai, yana kamfen ne domin zaben Sanata Tanko Al-Makura ya zama Shugaban jam’iyyar APC ( All Progressibes Congress) ta kasa.

Ya ce ya kasance yana tuntubar dukkan manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a duk fadin kasar a madadin tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Sanata Umaru Tanko Al-Makura da ke kan gaba wajen niman Shugabancin Jam’iyyar

Gwamna Sule, wanda ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan Gwamnati dake garin Lafia ya ce: “Yayin da muke ba da shawara cewa jam’iyyar ta yi adalci ga rusashiyar jam’iyyar CPC wajen zaben Shugaban APC na kasa da zai gudana nan gaba, ya kamata ayi la’akari da martabar jam’iyyar CPC da rawar da wannan bawan Allah Sanata Al-makura ya taka wajen kare martabar CPC da Shugaba Muhammad Buhari.

Ya ce “Don haka, nake yakin neman zabe gare shi, na kuma ba da shawarwari a matakai daban-daban na jam’iyyar; Na kasance tare da dukkanin manyan masu ruwa da tsaki na APC kuma munyi imanin cewa abin da muke nema adalci ne”.

Gwamna Abdullah Sule yace ba roko mukeyi ba muna bada shawara da kuma nuna cancanta ne ga jam’iyyar APC. Ya kara da cewa Na yi shawarwari, tare da yin magana da mutanen da suka dace waɗanda ya kamata su kasance cikin wannan tsarin.

“Ina magana da dukkan masu yanke shawara, ina tuntuɓar maɗaukakiyar ikon jam’iyyar a matakin ƙasa, musamman, ina magana da abokan aiki na, Gwamnoni, don duba Cancantar Sanata Umar Tanko Al-Makura saboda fari jinin da zai kawo wa jam’iyyar APC.

Ya cewa ba kawai yana neman a ba su mukamin shugaban jam’iyyar APC ta kasa a yankin Arewa ta Tsakiya ba ne, amma a ba jihar Nasarawa saboda rawar da ta taka a can baya.

Exit mobile version