Connect with us

RAHOTANNI

Sanata Aliero Ya Gabatar da Takardarsa Ta Tsayawa Takara A Karo Na Uku

Published

on

Tsohon Ministan Abuja, Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya gabatar da takardar tsayawa takarar kujerar sanatan Kebbi ta tsakiya, bayan ya kwashe shekaru biyu yana wakiltar wannan yankin a Majalisar Dattawan Nijeriya.

Kafin tafiyarsa Majalisar Dattawa, Sanata Adamu Aliero ya kasance tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, wanda a lokaci guda kuma ya kasance tsohon  Gwamnan jihar kebbi har karo biyu.

Jama’ar mazabun  Kebbi ta tsakiya sun tabbatar da bayar da goyon bayansu ga Sanata Aliero ta hanyar ba shi wata dama ta tsayawa takarar kujerar ta sanata mai wakiltar mutanen mazabar kebbi ta tsakiya a majalisar dattajai a zaben 2019 mai zuwa.

A jiya ne tsohon Ministan ya gabatar da takaradar neman takarar sa ne a sakatariyar ofishin jam’iyyar APC na jihar kebbi, wacce take da matsuguni a Birnin-kebbi.

Takardar wacce ya mika ta ga hannun shugaban jam’iyyar na jiha, Alhaji Bala Sani Kangiwa domin shuwagabannin jam’iyya a matakin jaha su tabbatar dashi cikin ‘yan takarar sanatocin jam’iyyar ta APC a jihar ta kebbi.

Yayin da Sanata Aliero  ya ke jawabi ga shuwagabannin jam’iyyar APC na jihar da kuma magoya bayan sa da suka bashi damar tsayawa takara karo na uku ya bayyana cewa; ”zan tabbatar da na yi muku wakilci mai inganci da kuma samar da gajiyar dimokradiyya fiye da wanda aka samar ga jama’a da kuma ciyar da kasar mu a mataki na gaba”.

Ya ci gaba da cewa a ci gaba da baiwa shugaba kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamna Abubakar Atiku Bagudu a kuma jefa musu kuri’a a zaben 2019 mai zuwa domin suka kara ciyar da kasar Najeriya a mataki na gaba .

Haka kuma yayi kira ga jama’a da su tabbatar da cewa sun mallaki takin zaben domin shi kada ne zaya baka ko baki damar zaben wanda kake so ko kika so.

Daga karshe ya godewa shuwagabannin jam’iyyar APC a na jihar da kuma mutanen mazabar kebbi ta tsakiya da irin damar da aka bashi na takara karo na uku a matsayin sanata mai wakiltar kebbi ta tsakiya a majalisar dattajai.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: