Sanata Dino Malaye: Zakaran Gwajin Dafi!

08148507210   mahawayi2013@gmail.com

Ga duk wanda ke bibiyar harkokin siyasar kasar nan yana sane da irin badakalar da ta faru, ko kuma in ce ke faruwa tsakanin Sanata Mai wakiltar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Malye da kuma rundunar ’yan sandan kasar nan, inda abubuwa suka yi tsami a tsakaninsu, wanda kuma wannan matsalar ke neman hada Shugaban ’yan sandan kasar nan da Majalsar Dattawan.

Tun farko dai lamura sun fara lalacewa ne sakamakon wasu matasa masu kai wa mutane hare-hare da rundunar ta kama a jihar Kogi, wadanda kuma ta ce ta samu bayani daga wgaresu cewa shi Sanata Dino Malaye ne ke daukar nauyin duk wasu harkokinsu, zargin da shi Sanatan ya musanta.

To amma tun bayan aukuwar lamarin sai ya zama ana ta samu bayanai masu karo da juna, inda wasu labaran ke cewa rundunar ’yan sandan tana neman Sanatan ruwa a jallo, sai kuma a samu wani labarin da ke cewa an ga Sanatan ya sauka jiharsa ta Kogi bisa rakiyar jami’an tsaron. Har ma wasu lokuta akan ce an ga jami’an tsaron a gidansa na Abuja suna bincike.

Ana cikin haka ne sai kwatsam aka sami labarin cewa ga jami’an ’yan sandan can sun zagaye gidan Sanatan, kafin daga bisani kuma aka ce an kama shi, bayan sun kammala binciken. A wannan kamen ne rahotanni daga rundunar ’yan sandan ta ce shi Sanata Dino ya yi yunkurin kashe kansa ta hanyar dirowa daga motar da ake tafiya da shi don hukunta shi.

Rahotanni sun suna cewa Dino Malaye ya samu munanan raunuka sakamakon wannan dirowa da ya yi, wanda ake zargin ya diro ne domin ya tsere daga hannun ’yan sandan a kan hanyarsu ta tafiya garin Lokoja da shi. Amma shi kuma Sanata Dino ya bayyana cewa ya diro daga motar ne don ya tsira daga kisan gillar da yake zagin ana niyyar yi masa.

Sakamakon raunukan da ya samu a wannan rana, sai da aka garzaya da shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja mai suna Zanklin Hospital.

Wasu abubuwa sun faru a lokacin da Dino ke asibitin, inda Majalisar Dattawan da aika da wani kwamiti don ya gana da shi, amma aka ce jami’an ’yan sada sun hana kwamitin shiga inda yake, matakin da ya tilasta wa Shugaban Majalisar, Sanata Bukulo Saraki, bisa rakiyar da dama daga cikin Sanatocin zuwa da kansu asibitin don ganawa da da shi Dinon, kuma sun shiga sun gana da shi.

Ita rudunar ’yan sandan ta bayyana cewa ta yi niyyar tafiya da Dino ne zuwa Lokoja domin hada shi da wadancan matasan da ta kama bisa zargin aikata nunanan ayyuka, cikinsu kuwa har da wani da aka sake cafkewa bayan da ya gudu daga hannun jami’an tsaron.

Wannan kamu da aka yi wa Sanatan ya zama wani abu da ba za a taba mantawa da shi ba, musamman ganin cewa ba a taba yi wa wani mai matsayi irin na Dino irin wannan tozartarwa ba, musamman yadda aka sanya masa Ankwa, tamkar dai wani dan ta’adda, kuma matakin da bai yi wa Majalisar Dattawan dadi ba.

Kamar yadda na bayyana a sama, rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa ta yi wa Sanata Dino wannan kamu ne domin ta kai shi gaban kuliya bisa zargin da take yi masa na taimaka wa wasu matasa ’yan bangar siyasa, wadanda kama a kwanakin baya ake zarginsu da kashe-kashen jama’a a jihar ta Kogi.

Ba a wannan karon ba ne rundunar ‘yan sanda ta ke tuhumar Sanatan bisa wannan zargi ba, domin ko a watannin baya ma ta yi masa wasu tambayoyi bisa wannan zargi, kodayake bayanai sun nuna cewa Sanata Dino ya ki amsa gayyatar da aka yi masa, bisa zargin cewa ba shi da amincin shiga Lokoja.

Akwai ma lokacin da jami’an Kwastan suka taba tsare Sanata Melaye, kuma suka sake shi a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe international airport. Haka kuma ya taba rubutawa a Soshiyal Midiya yadda jami’an ’yan sanda suka mamaye gidansa da ke Abuja.

Domin ya taba rubutawa a shafinsa na twitte, @dino_melaye, cewa “an rufe duk hanyoyin da ke zuwa gudana, ’yan nsanda kwantar da tarzoma ne dauke da muggan makamai suka fufe hanyar shiga da fita. Yanzu haka sun mamaye ciki da wajen gidan nawa.” A lokacin da ya yi wannan bayanin.

Ga dukkan alamu wadannan abubuwa da ke faruwa tsakanin rundunar ’yan sandan da Sanata Dino Melaye ya harzuka Majalisar Dattawan, wanda kuma wannan harzukawa ta jawo zazzafar matsala tsakaninta da Shugaban ’yan sandan, Ibrahim Idris domin ta gayyace shi ya bayyana a gabanta, amma ya ki bayyana, bayan sammacin da ta yi masa har sau hudu, amma bai masa ko daya ba.

Jama’a da dama na ganin cewa Majalisar na neman Shugaban ’yan sandan ne bisa cin zarafin da suke zargin an yi wa dan nasu, amma ita Majalsiar ta nuna cewa tana nemamsa ne domin ya zo gabanta ya kare kansa bisa kashe-kashen da ke faruwa a sassan kasar nan da har yanzu an kasa magance su. Wanda har ta yi zargin cewa sam bai kamata Ibrahim Idri ya rike babban matsayi irin na Shugaban ’yan sanda ba.

Bayan wannan badakala da Sanata Dino ya yi ta fama da ita tsakaninsa da ’yan sanda, wacce sai da ta kai ma yanzu haka yana hannu, akwai kuma rikicin da ya yi fama da shi na barazanar tsige shi ta hanyar kiranye daga mazabarsa, shirin ya da ya yi zargin abokan hamayyarsa ne, musamman Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ke kitsawa.

An yi ta kai ruwa rana a wannan batu, wanda har ta kai ma ita Hukumar zaben ta yi ta bayanai a kai. Amma a halin da ke ciki dai shi wannan batu na kiranye babu shi, domin Hukumar zaben ta yi wa tukka hanci.

Irin wadannan abubuwa da suke samun Dino Melaye suna daukar ra’ayoyin jama’a da dama, inda kuma wadannan ra’ayoyi ke bambanta. Wasu na ganin cewa halin Dino ne ke ja masa wadannan abubuwa, wasu na ganin cewa rikicinsa ne da Gwamnan jiharsa ya sa yake samun wadannan matsaloli. Wasu kuma na ganin cewa ai idan sauran Sanatoci ba su yi a hankali ba, to Dino zai zama zakaran gwajin dafi ne, abin zai iya zuwa kan kowa daga cikinsu.

 

Exit mobile version