Umar A Hunkuyi" />

Sanata Dino Melaye Ya Bayyana Aniyarsa Ta Yin Takarar Gwamnan Jihar Kogi

Sanata Dino Melaye, mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma, ya shelanta aniyarsa ta tsayawa takaran gwamnan Jihar Kogi a zaben gwamnan Jihar da aka shirya gabatarwa a ranar 16 ga watan Nuwamba. Melaye ya bayyana aniyar na shi ne jiya lokacin da ya tattauna da shugabannin Jamíiyyar PDP a mazabar Kogi ta yamma, wanda aka yi a garinsu da ke Aiyetoro Gbede, ta karamar hukumar Ijumu, ta Jihar.

A lokacin da Sanatan yake neman goyon bayan shugabannin jamíiyyar, ya nuna tabbacin da yake da shi na zama gwamnan Jihar. Mai taimaka masa a kan harkokin manema labarai, Gideon Ayodele, ya tabbatarwa da manema labarai hakan a ranar Lahadi, inda ya ce shugaban na shi ya shelanta aniyar na shi ta tsayawa takaran a lokacin da ya gana da shugabannin jamíiyyar a mazabar ta Kogi ta yamma wanda aka yi a gidan Janar Dabid Jemibewon da ke Aiyetoro Gbede.

Exit mobile version