Khalid Idris Doya" />

Sanata Gumau Ya Raba Buhun Shinkafa 710 Ga Masu Azumi A Mazabarsa

Sanatan da ke wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu a majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Lawan Yahaya Gumau ya kyautar da buhun shinkafa guda dari bakwai da goma (710) ga al’ummar Musulmai da suke karkashin mazabarsa a cikin kananan hukumomi bakwai da suke jihar Bauchi domin su samu zarafin jin dadi da walwala a cikin watan Ramadanan da muke ciki.

Gumau ya shaida adadin buhun shinkafar da ya rabar ne a lokacin da ya kaddamar da rabar da kayyakin ga wadanda Allah ya sa suka ci gajiyar kyautar a ofishin Mazabarsa da ke Bauchi.

Ya shaida cewar baya ga shinkafar akwai kuma wasu daga cikin kayyakin da ya rabar da suka hada da yadunan Shadda da Atamfofi ga maza da mata domin kyautata wa jama’a a cikin watan Azumi.

Sauran kayakkin da ya rabar din sun hada da Atamfa guda 300 da aka rabar wa mata, yadunan Shadda guda dari uku da aka rabar ga maza don su samu kayan dinkawa a ranar Sallah.

Baya ga nan, ya kuma nemo Daraktocin yakin neman zabensa da kuma Ko’odinetocinsa da suke fadin kananan hukumomi bakwai su dari da hamsin ya samar musu da kyautar naira dubu goma-goma da yadunan shadda guda biyar-biyar ga kowannensu domin gudanar da shagulgular sallah cikin annashuwa.

Ya ce; “Al’umma a cikin karamar hukumar Bauchi sun samu cin gajiyar buhu shinka 50, yadunan zanin dinkawa na mata da shadduna guda sittin, a karamar hukumar Toro kuma, sun samu buhun shinaka dari da ashirin da kuma shadduna da zanin mata guda hamsin, a karamar hukumar Alkaleri na rabar da buhun shinkafa dari da ashirin da kuma shadduna da yaduna guda dari,”

Ya ce, sauran kananan hukumomin da suka amfana da tallafin nasa sun hada da karamar hukumar Tafawa Balewa wacce ta samu kyautar buhun shinka dari da ashirin, shadduna da yaduna guda 100 wadanda aka raba wa musulmai kyauta a cikin watan Ramadan, Inda a karamar hukumar Kirfi kuwa ya rabar da kyautar buhun shinkafa dari da goma da kuma basu kyautar shadda da ataffa guda saba’in.

Ya shaida cewar ya yi hakan ne domin dadada wa al’ummar da suke mazabarsa, ya nemi musulmai da su yi amfani da watan Ramadana wajen yin addu’a wa kasa da ci gaban zaman lafiya a fadin Nijeriya.

Exit mobile version