Daga Khalid Idris Doya,
Sanata Lawal Yahaya Gumau, mai wakiltar Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawa ta Nijeriya ne ya raba kyautattukan sabbin motoci guda shirin da bakwai (27) mafi yawancin su kirar Siyana wa kungiyoyin addinai da ke cikin mazabarsa.
Bikin kyautar motocin, wanda aka gudanar a garin Magamar Gumau dake cikin karamar hukumar Toro, ya samu halartar mabiya addinan Musulumci dana Kiristanci, hadi da ‘yan siyasa, wadanda suka yi ta yabawa kokarin Sanatan.
Da ya ke jawabi a wajen bikin, wakilin Sanatan a wajen rabiyar, Alhaji Aminu Abubakar Dawaki ya bayyana Sanata Lawal Gumau a matsayi mutum mai jin kai, mai kyauta, kuma mai bibiyar lamuran jama’a, wanda ya yi fice wajen raba ribar dimokaradiyya wa jama’a.
Dawaki, wanda ya yi la’akari da cewar, fagen siyasa a share yake tarwal wa Sanata Gumau wanda ya inganta rayuwar dubban jama’a ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa kamar rijiyoyin burtsatse, ajujuwan makarantu, wutar lantarki, karfafa mata da matasa, samar wa matasa ayyukan soji, dan-sanda, kastam, imagireshin, dogarancin hanya, da samar wa matasa makarantu, dadai sauran su.
Alhaji Aminu Dawaki, don haka ya yi kira ga daukacin jama’ar mazabar sanatan dake cikin kananan hukumomin Bauchi, Toro, Alkaleri, Kirfi, Tafawa Balewa, Dass da Bogoro dasu baiwa Sanatan dukkan goyon baya daya dace kan fafitikar sa ta tsamo jama’a daga kangin talauci, jahilci, cutattaki da kuma ‘yunwa.
Dawaki sai ya bayyana cewar, rabon karfafa jama’a da sanatan zai yi nan bada jimawa ba, kuma wanda shine kashi na uku na makamancin hakan, ya hada da rabon motoci guda 120 da babura guda dubu daya, hadi da wasu kayayyakin more rayuwa, yana mai cewar, Sanatan ya jima yana tallafawa inganta rayuwar jama’a.
Rabaran Jaja S. Dangi wanda tsohon jami’i ne a hukumar jin dadin masu Urshalima da yake cikin kungiyar addinin kiristanci a karamar hukumar Toro da suka amfana da tallafin, wanda kuma ya yaba wa Sanata Gumau bisa wannan tagomashi, yana mai cewar, motar zata taimaka wajen gudanar da lamuran addinin su.
Rabaran Jaja Dangi sai ya bayar da tabbacin cewar, kungiyar su za ta cigaba da baiwa sanatan shawarwari, tare da yi masa addu’o’in samun nasara a cikin gwagwarmayar sa ta siyasa, yana mai cewar, ba wata abu bace siyasa face zaman lafiya, cudanya da juna da kuma hadin kai domin cimma manufofi.
Shi ma da yake jawabi a wajen taron, jagoran kungiyar JIBWIS a karamar hukumar Toro, Muhammad Abdullaji Jajuwal ya jinjina wa Sanata Lawal Gumau wanda, ya ce, yana tallafa wa kungiyoyin addinai dake cikin karamar hukumar, don haka ya yi masa fatar alheri.