Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya: Jajirtaccen Wakilin Da Babu Kamarsa

by
4 years ago
in SIYASA
5 min read
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya: Jajirtaccen Wakilin Da Babu Kamarsa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

2023: Takarar Shugaban Kasa Ba Dole Ne Sai An Yi Karba-Karba Ba — Sarkin Ooni Na Ife

Adamawa: Ban Janye Wa Kowane Dan Takara Ba – Fwa

ADVERTISEMENT

Wakilicin al’umma dace ne kamar yadda Hausawa kan fadi, wannan ta sa a duk lokacin da al’umma suka yi sa’ar zabar jajirtaccen wakili, dan Kisihin kasa da al’ummarta, Masanin Makamar aiki, Jarumi mara tsoro mai kyakkyawan dogaro ga Allah, babu shakka wannan al’umma zasu ci gaba da kwankwadar romon wakilcin da suka tura a kowane irin mataki.
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya Shi ne Sanata mai Wakiltar Kano ta Kudu, mazabar da ta zarta daukacin mazabun sanatocin dake fadin afirika baki daya, Kabiru Gaya na wakiltar wannan mazaba mai kananan Hukumomi goma sha shida. Wannan ta sa dole aikinsa ya bambanta da na sauran, sannan kuma irin wannan mazaba na bukatar gogaggen dan siyasa mai kaunar cigaban al’ummar da ya fito daga cikinsu.
Kamar yadda duk wanda ya kwana kuma ya tashi a yankin mazabar Kano ta Kudu ya san sunan da ake kiran wannan bawan Allah dashi na Baba Mai Sola, wannan yana daya daga cikin abubuwan da Kabiru Gaya ya banbanta sauran Sanatocin da suka fito daga Jihar Kano, domin samar da rijiyoyi masu amfani da hasken rana, abin ya zama kamar ruwan dare gama duniya, ba wai mazabarsa kadai ba kusan sai da ta kai jama’a daga sauran mazabun na kwarara zuwa gareshi domin rokon suma a taimake su da ire iren wadanann rijiyoyi, kuma duk wadanda suka kai koken sai ya share masu hawaye. Al’ummar Kasuwar Kantin Kwari na cikin jama’ar da basa mantawa da hidimar Kabiru Gaya, domin har maganar da ake ahalin yanzu da rijiyoyin masu amafani da hasken ranar da ya samar a kasuwar suke
amafani.
Yana daga cikin kudurinsa na samar da kyakkyawan wakilci, inda yake gabatar da kudurori wadanda suke inganta makomar al’ummar kasar nan tare da amfanar romon dimokaradiya, wannan tasa Kabiru Ibrahim Gaya ne mutum na farko daga Najeriya a ya taba rike gwaggwaban mukami a Kungiyar ‘yan Majalisun dokoki na afirika baki daya (IPU) wadda aka kafa a shekara ta 1989, Kabiru Gaya ya tabbatar da cewa zai yi aiki ka’in da na’in domin tabbatar da hadin kan ‘yan majalisun afirika wajen daukar matakin kan abubuwan da zasu kyautata rayuwar al’ummar wannan yanki.
Domin tabbatar da cigaban al’ummar mazabarsa, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya mayar da hankali wajen samar da kayan kiwon lafiya masu inganci, ciyar da harkokin ilimi domin amfanin masu karamin karfi, bayar da tallafin harkokin noma ga Manoma, samar da gurabun aiki ga matasa da kuma ayyukan raya kasa a Kananan Hukumomi 16 da yake wakilta. Haka kuma Sanata Gaya ya yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da daga darajar al’ummar Kano ta Kudu.
Wannan tasa yake aiki ba dare ba rana domin ganin ayyukan da ake na harkokin lafiya kyauta ga mutanen mazabar Kano ta Kudu na haifar da kyakkyawan sakamako. Haka kuma Kabiru Gaya na daukar nauyin ayyukan da jinya da suka fi karfin talaka, sai kuma bayar da tallafin dubban gilasai ga mutane masu matsalolin ido duk kyauta.
Domin tabbatar da samar nagartaccen ilimi Sanata Kabiru Gaya ya baiwa bangaren ilimi kulawar musamman, inda ya bayar da gwaggwabar gudunmwa
ga jama’ar yankinsa, ya gina Ajujuwa sama da 450 tare da gina wuraren kewaya ga dalibai a daukacin kananan Hukumomin da ke karkashin mazabarsa 16, sannan kuma yana baiwa harkar gyara saura ajujuwan da suka jima a lalace kulawar gaggawa domin ganin an ci gaba da amfani dasu.
A dai kokarinsa na tabbatar da kyakkyawan wakilci Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya gina cibiyoyin Na’ura mai kwakwalwa a kananan Hukumomin Rano da Gaya tare da gwangwaje su da kayan aiki wanda aka sadar dasu da sauran kananan Hukumomin da ke wannan mazaba tasa domin samun saukin gudanar da bincike da kuma harkokin cigaban zamani.
Kamar yadda ya zama halayarsa ta kyautatawa harkokin ilimi, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na sayen fam domin amfanin daliban dake bukatar zana jarrabawar sakandire har da masu bukatar fadada karatunsu zuwa makarantun gaba da sakandire suma suna amfana da wannan tagomashi nasa. Gaya ya kuma gina ajujuwa uku-uku a Dundun karamar Hukumar Gaya, Makarantar Sakandire ‘yan mata a Faragai karamar Hukumar Albasu, Makarantar Sakandire a Gaya, JGSS Autan Bawo a Karamar Hukumar Rano, GGS Rogo, GSS Sumaila, GSS Rimi, GSS Garko, GSS Rahama, GSS Bebji, GSS Kibiya. GSS Bunkure, GSS Takai da sauransu.
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya dan siyasa ne Mai tsari, wanda baya tsoron bayyana ra’ayinsa akowa da yaushe, wanda yace za’a ci gaba da tuna shi kasancewarsa guda cikin turakun da suka kafa Jam’iyyar APC. Gaya na cikin Sanatocin da su ka fi nuna Kwarewa, tsohon mataimakin marasa rinjaye, shugaban kwamitin Jihohi da Kananan Hukumomi a wani lokaci a can baya.
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ganin yadda ya dau harkokin hanyoyin da muhimmancin gaske wanda ingancinsu ke tabbatar da saukaka hakokin zirga zirgar al’umma. Mai Girma Sanata ya yi kokarin gabatar da kudurin samar a gadar sama a Kundila da kuma gadar Silber Jublee a
shekara 2009. Sai kuma gina gadar da ta hade Kananan Hukumomin Tudun wada – Doguwa, sai kuma yadda ya taimaka wajen gyaran gadar Wudil.
Sanata Gaya ne ya samar da aikin gadar Turawa a karamar Hukumar Karaye, gadar Unguwar Tofa a Karamar Hukumar Karaye, Gyara wurin shakatawa na Falgore a karamar Hukumar Doguwa, hanyar Gaya – Balare zuwa Ringim, Gyara titunan cikin garin Gaya, sai kuma hanyar data hade Kafin Mai yaki- Tudun Wada-Doguwa zuwa iyakar Kano da Kaduna.
Inganta samar da ayyukan raya kasa da Sanata Kabiru Gaya ke aiwatarwa ne ke zaman abubuwan tattaunawa a tsakanin al’umma wadanda ake kare maunfofinsu a matakin kasa da Sanata Kabiru Gaya ke gudanarwa.
Cikin Manyan Nasarorin da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya samu musamman kasancewarsa Shugabban Kwamitin ayyuka na Majalisar dattijai ne ya bashi damar gabatar da kudurin kafa hukumar lura da yankin arewa maso gabas a shekara ta 2015, wanda wannan hukuma ta zo a lokacin da ake bukatarta. Gaya ya bayyana cewa samar da wannan hukuma zai bayar da damar dakile kalubalen da al’ummar yanki ke fuskanta musamman matsalar Boko Haram wadda ta addabi Jihohin Boro, Yobe da Adamawa, inda dubban al’umma aka raba su da gidajensu.
Wani babban aiki da za a bugi kirji a ce Sanata Kabiru Gaya ya nemo, shi ne, sake gina babban hanyar da ta tashi daga Kano ta ratsa Zariya, zuwa Kaduna hart a isa birnin tarayya Abuja. Wannan gagarumin aiki da aka kaddamar kwana baya, zai taimaka kwarai da gaske wajen bunkasa tattalin arziki Najeriya musamman Arewa duba da yadda hanyar ta hada kusan dukkanin jihohin Arewa da Kudancin kasar nan. Har ila yau, gyaran hanyar zai rage asarar rayuka da ake samu ta dalilin hadura, sakamakon ramukan da suka cika titin.
Baya ga wannan, Sanata Kabiru yana da hannu a kusan gyaran manyan tituna da ake yi a Najeriya, a matsayinsa na shugaban Kwamiti a Majalisar Dattawa na gyaran hanyoyi, ya jajirce matuka da gaske wajen ganin titunan kasar nan dawo hayyacinsu.
Haka Kuma a wani cigaban da Sanata Gaya ya samu wanda ya yiwa masu rajin kusanci da shugaban Kasa Muhammadu Buhari kurunkus, shi ne yadda shugaban ya jinjinawa Sanata Kabiru Gaya bisa zabarsa a matsayin mataimakin shugaban kungiyar hadin kan ‘Yan Majalisun dattijai na afirika, zaben da ya gudana a watan nuwambar shekara ta 2016, Jawabin na shugaban kasa wanda mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar yace Gaya na da gogewa, kwarewa da kuma karsashi yiwa wannan kungiya hidima.
Shugaban Muhammadu Buhari ya bukaci Sanata Kabiru Gaya da ya tabbatar da ciyar da wannan kungiya gaba ta hanyar kyakkyawar demokaradiyyar da ke wanzuwa, Buhari yace ina da tabbacin cewa Gaya zai iya gudanar da wannan muhimmin aiki.
A siyasance, Sanata Kabiru Gaya yana da kyakkyawar alaka da mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Har ila yau, tuni ta bayyana karara kan irin goyon bayan da yake bai wa Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, musamman irin kokarin da yake yi na ganin jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe zabukan da da za a gudanar a shekarar 2019.
An haifi Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ranar 6th ga watan June na shekara ta 1952, gogaggen dan siyasa, kwararren mai zaben kasa, wanda aka zaba a matsayin Sanata a shekara ta 2007 mai wakiltar Kano ta Kudu daga Jihar Kano karkashij tutar Jam’iyyar APC, Gaya ne Sanata mai wakiltar mazabar da tafi dukkan mazabun dake fadin Afirika fadi.
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya samu digiri na farko a fannin harkokin zane daga Jami’ar Ahmadu Bello Zaria a shekara 1977, sai kuma digir harda digir digir adai jami’ar Ahmadu Bello Zaria a 1980. Sannan aka bashi digirin girmamawa wadda Jami’ar kimiya da harkokin gudanarwa ta Porto-Nobo a Benin ta bashi. Wakili a kungiyar masu zane ta kasa (NIA) da kuma kungungiyar manyan Manoma (NLSFA). An zabi Sanata Gaya a matsayin Gwamnan Kano a shekara ta 1992 zuwa 1993, A shekara ta 2003 Kabiru Gaya ya tsaya takarar Gwamna a karkashin tutar Jam’iyyar NDP.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Hukumar NIS Ta Musanta Kama Bakin Haure A Jihar Kogi

Next Post

Ban Ji Dadin Abin Da Ya Faru Ga Kasashen Afirka Ba A Kofin Duniya, Cewar Shugaban FIFA

Labarai Masu Nasaba

2023: Takarar Shugaban Kasa Ba Dole Ne Sai An Yi Karba-Karba Ba — Sarkin Ooni Na Ife

2023: Takarar Shugaban Kasa Ba Dole Ne Sai An Yi Karba-Karba Ba — Sarkin Ooni Na Ife

by Abubakar Abba
4 hours ago
0

...

Adamawa: Ban Janye Wa Kowane Dan Takara Ba – Fwa

Adamawa: Ban Janye Wa Kowane Dan Takara Ba – Fwa

by Muh'd Shafi'u Sale
5 hours ago
0

...

Mataimakin Kakakin Majalisar Bauchi Ya Sha Kaye A Zaben Fid Da Gwani

Mataimakin Kakakin Majalisar Bauchi Ya Sha Kaye A Zaben Fid Da Gwani

by Khalid Idris Doya
5 hours ago
0

...

Shugaban Majalisar Dattijai

Zan Cigaba Daga Inda Buhari Ya Tsaya – Lawan

by
16 hours ago
0

...

Next Post
Ban Ji Dadin Abin Da Ya Faru Ga Kasashen Afirka  Ba A Kofin Duniya, Cewar Shugaban FIFA

Ban Ji Dadin Abin Da Ya Faru Ga Kasashen Afirka Ba A Kofin Duniya, Cewar Shugaban FIFA

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: