Abubakar Abba" />

Sanata Lado Da Magoya Bayansa Sun Koma PDP A Katsina

Tsohon dantakar jamiyyar (PDM) a jihar Katsina a zaben 2015 Sanata Yakubu Lado Danmarke tare da dubban magoya bayan sa sun canza sheka zuwa jamiyyar  (PDP).

Shugaban PDP na kasa Uche ne ya karbe su a taron gangami da PDP ta gudanar na shiyar Arewa maso Yamma Katsina cikin satin da ya gabata.

Secondus a jawabin sa a wurin taron da dubban magoya bayan PDP da suka fito daga shiyyar da kuma na kananan hukumomin jihar 34  dake Katsina, ya bayyana jin dadin sa akan komawar shahararren dan siyasar Sanata da kuma dubban magoya bayan sa, inda yace, hakan ya karawa PDP karfi kafin zuwa zabubbukan 2019.

Secondus ya kara da cewa, wadanda suka canza shekar zasu amfana da dukkan damar da PDP ta tanadar kamar na  sauran tsofaffin ‘yan PDP kuma ba wanda zai nuna masu wani banbanci.

Acewar sa, a matsayin mu na ‘yan shine tabbatar da daukacin ‘yan Nijeriya sun amfana da PDP. ”

Yaci gaba da cewa, ganin yadda alummma suka fito kwansu da kwar-kwatar su, alamu ne dake nuna cewar, PDP a shirye take don karbar shugabanci a Katsina da kuma shugabancin Nijeriya a zabubbukan da za’a gudanar a 2019”.

Ya yi nuni da cewar, idan aka zabi PDP zata zage wajen samarwa da ‘yan Nijeriya aminci, inda kuma ya yi zargin cewar, APC tazo ne kawai don ta yada yunwa da talauci da munafurci a kasa.

Da yake nashi jawabin a madadin wadanda suka canza shekar, Sanata Lado ya yi alkawarin yin dukkan mai yuwa don tabbatar da PDP ta karbe madafin iko daga gun APC a Katsina da kuma a tarayya.

Lado ya kuma yi kira ga daukacin ‘yayan PDP dasu zama tsitsiya madauri daya don tsomo kasar nan daga cikin matsalolin da take fuskanta, inda kuma ya yi alkawarin cewar, PDP zata samarwa da ‘yan Nijeriya wadataccen tsaro da farfado da tattalin arzikin kasa da kuma inganta

rayuwar su.

Wadanda suka halarci taron sun hada da; gwamnonin jiharGombe da Ekiti da Akwa- Ibom.

Sauran sun hada da; tsohon gwamnan Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema da tsohon gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamido da tsohon gwamnan  Kano, Malam Ibrahim Shekarau da tsohon gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru.

 

Exit mobile version