Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya lashe kyautar shugabanci ta Zik ta shekarar 2019, wadda a ka fi sani da ‘2019 Zik Prize in Political Leadership’.
Bayanin hakan ya na kunshe ne a takardar manema labarai, wadda mai taimaka wa shugaban majalisar kan aikin jarida, Malam Mohammed Isa, ya sanya wa hannu, ranar Litinin.
Da ya ke karbar kyautar, Sanata Lawan, wanda shugaban ma’aikata a ofishin shugaban majalisar, Dr Babagana Muhammad-Aji ya wakilta a kasaitaccen bikin da ya gudana a ranar Lahadi, a birnin Legas.
Mohammed Isa ya ce an zabi shugaban majalisar ne bayan dogon nazari da cikakken binciken kwakwaf da cibiyar ‘Public Policy Research and Analysis Centre’ (PPRAC) ta gudanar, wanda a karshe ta zabi shugaban majalisar dattawan, ta la’akari da gudunmawar da ya bayar a fannin hidimta wa Nijeriya na tsawon lokaci, tare da irin jajircewar sa wajen tabbatar da cigaban tsarin dimukaradiyya.
Sanata Lawan ya ce ya sadaukar da kyautar ga abokan aikinsa a zauren majalisar saboda yadda suka nuna bajintar kawar da bambancin siyasar da ke tsakanin su domin ganin an samu cigaban Nijeriya.
“Saboda yadda wannan kyautar ta samu ne ta dalilin cikakken goyon bayan da abokan aikina su ke bani, duk da irin bambance-bambancen da ke tsakaninmu a siyasance.
“Bugu da kari kuma, ko shakka babu wannan kyautar zata kara min kwarin hwiwa tare da sauran yan majalisar da mu ke aiki tare, wajen fuskantar aikinmu, sannan da bayar da himma da tabbacin cigaba a fannin kokari wajen gina kasa.”
Kyautar ‘Zik Price’ dai an kafa ta ne a 1994, domin girmama Shugaban Nijeriya na farko, Dr Nnamdi Azikwe, don samar da kwarin gwiwa da shugabanni a nahiyar Afrika.
A hannu guda kuma, hazikan mutanen da su ka taba samun wannan kyautar a shekarun baya sun hada da Jerry Rawlings a1995, Julius Nyerere a 1997, sai Dr Nelson Mandela a 2000, Yonweri Muzebeni a 2003, John Kuffor a 2008, Alhaji Yayale Ahmed a 2010, Ellen Johnson Sirleaf a 2011, a Afe Babalola a 2013, Hon. Yakubu Dogara a 2015, Alhaji Ahmed Joda a 2016, Chief Audu Ogbeh a 2017 da Farfesa Ayo Ibidapo-Obe a 2018, sai kuma Sanata Ahmad Ibrahim Lawan a 2019.