Abubakar Abba" />

Sanata Lawan Ya Nuna Takaici Kan Rashin Bincike A Fannin Noma

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya nuna takaicin sa karara kan yadda masu bincike a fannin aikin gona a Nijeriya su ka gaza yin kokarin a zo a gani wajen gudanar da buncike a fannin a Nijeriya duk da kokarin da kasar nan take yi na kara wadata Nijeriya da abinci mai dinbin yawa.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya sanar da hakan ne a zauren Majalisar dake a babban birnin tarayyar Abuja a yayin da yake yin dubi kan kudurin Cibiyar godanar da bincike a fannin aikin noma ta kasa ARCN don sabunta kudurin zuwa doka a wani karamin zaman da Majilisar ta yi.

Sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Yamma Abdullahi Adamu kuma tsohon gwamnan jihar ta Nasarawa ne ya gabatar da kudurin  don kara habaka Cibiyar ta gudanar da bincike a fannin na aikin noma na kasar nan.

Sai dai, Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya danganta rashin yin amfani da fasahar zamabi a fannin aikin noma a kasar nan a matsayin daya daga cikin matsalolin dake ciwa manoman kasar tuwo a kwarya.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya kara da cewa. Gabin yadda ake da kwararrun cibiyoyin gudsnar da bauncike a fannin aikin noma guda 23, ya kamata ace kasar nan za ta iya bunkasa fannin aikin gona ta hanyar kimiyyar zamani.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya kara da cewa, bai dafe ace har yanzu manoman Tumatir a kasar nan sai sun shanya Tumatir ko Tattasan da suka noma ya sha rana  kafin su sayar dashi ba, inda ya sanar da cewa, mafi yawancin su suna shanya shi a kan titi ko a wani wuri kafin ya bushe su sayar da shi ba, wanna ba za ta taba sabuwa ba.

A cewar Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya kamata a kalla a dinga yin amfani da fasahar zamani wajen yin noma a kasar nan mai sauki, musamman don a taimakawa manoman da ke kasar lallai sai an yi amfani da babbar fasahar zamani ba.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya kuma kara jaddada bukatar ssmarwa da fannin wadatattun kudade, inda ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya ta kebewa fannin aikin gona naira biliyan 183.08 ne kacal a cikin kasafin kudinta na na wannan shekarar wanda a kai kashi 1.73 a cikin dari na jimlar kasafin kudi daga cikin naira sama da naira tiriliyan 10.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya kara da cewa, muna bukatar a zuba judade da yawa a fannin aikin gona na kasar nan, musamman don baiwa hukumomin aikin noma da zasu iya yin wani abin azo a gani.

Shi ma a nasa bangaren, Sanata dake wakilitar mazabar Nasarawa Yamma Abdullahi Adamu ya ce, kudurin da ake son ya zamo dokar, zai taiamakawa Cibiyar ta gudanar da bincike a fannin aikin noma matuka in ya zamo doka.

A karshe, Sanatan dake wakilitar mazabar Nasarawa Yamma Abdullahi Adamu ya ce, fannin aikin noma yana bayar da gagarumar gudunmwa wajen habaka tattalin arzikin kasar nan kuma yana samar da kimanin kashi 21 a cikin dari na arzikin Nijeriya.

 

 

Exit mobile version