Daga Muh’d Shafi’u Saleh
Sanata Ishaku Abbo, wanda ke wakiltar Arewacin Jihar Adamawa a Majalisar Dattawa a jam’iyyar PDP mai mulkin jihar, ya koma jam’iyyar APC mai adawa.
Da ma dai anjima ana takunsaka tsakanin sanata Abbo da gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri, duk da cewa ‘yan jam’iyya guda ne da su ka fito ne daga yanki guda.
Jama’a da dama a Yola fadar jihar, ba su yi mamaki da jin cewa ya fice daga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ba, duba da sanin yadda su ka kai ruwa rana da gwamna Fintiri.
Ficewar sanatan daga jam’iyyar PDP na zuwa ne, watanni da ficewar tsohon gwamnan jihar Bala James Ngillari, daga jam’iyyar.