Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

Sanata Misau Ya Nuna Farin Cikinsa Ga Matakin Hukumar ‘Yan Sanda

by Tayo Adelaja
September 12, 2017
in MANYAN LABARAI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga  Musa Muhammad, Abuja

A karshen makon da ya gabata ne Hukumar Harkokin ‘Yan Sanda ta tabbatar da cewa Sanata Isah Hamma Misau, mai wakiltar shiyyar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ya bi ka’idojin ajiye aikin dan sanda kafin ya tsunduma cikin harkokin siyasa.

samndaads

A yayin da yake zantawa da manema labarai, jim kadan bayan da hukumar ‘yan sandan ta goyi bayansa cewa ita ce da kanta ta ba shi takardar ajiye aikin a ofishinsa dake Abuja, ya nuna farin cikinsa bisa abin da ya kira bayyanar gaskiya, sannan ya ce da ma rundunar ‘yan sandan ta yi amfani da wannan dabara ce domin shashantar da zargin almundahanar da ake mata, wanda kuma gaskiya ne.

Idan za a iya tunawa, bayan dai daukar lokaci mai tsawo ana musayar kalamai tsakanin rundunar ‘yan sandan da kuma Sanata Misau, rundunar ta ayyana cewa ta na nemansa ruwa a jallo bisa laifukan arcewa daga bakin aiki da kuma tsunduma harkokin siyasa ba bisa ka’ida ba.

Ya kuma ce Sanata Isa Misau ya zargi shugaban rundunar ‘yan sanda da karbar cin hanci kafin tura kwamishinoni zuwa jihohin da aka fi samun alherin ofis, tare da karkatar da wasu kudaden kimanin naira biliyan 10 duk wata, da yake karba daga wasu kamfanonin dake amfani da ‘yan sanda zuwa aljihunsa maimakon lalitar gwamnati.

Mashood ya kuma ce wannan zargi na Sanata Misau labarin kanzon kurege ne kawai, inda ya ce haka kawai sanatan ya daina zuwa aiki tun a ranar 24 ga Watan Satumbar 2010, sakamakon canjin wurin aikin da aka yi masa, wadda bai yi ma sa dadi ba.

Ya kuma kara da cewa takardar barin aikin da dan majalisar ya nuna ga manema labarai su a wurin su ta jabu ce. Rundunar ta kuma ce ta na neman sanatan ne ruwa a jallo don ya zo ya yi mata bayani dalla-dalla kan dalilin da ya sanya ya daina zuwa aiki ba tare da wani kwakwaran dalili ba.

Sai dai da yake mai da martini, Sanata Isa Hamman Misau ya ce shi bai gudu ba, yana nan kamar yadda rundunar ‘yan sandan ke zargi, ya na mai cewa rundunar ta na kokarin karkatar da hankulan al’ummar Najeriya ne daga abin da ake zarginta da shi.

Inda ya ce idan ba haka ba, me ya kawo maganar cewa har yanzu shi dan sanda ne, bayan da ya cike ka’idojin ajiye aiki tun a shekarar 2010, kuma ya biya hukumar kula da ‘yan sanda kudin barin aiki wajen sadaukar da albashinsa na wata guda akan naira dubu 120 a lokacin da ya bar aikin.

A farkon wannan makon ne dai wannan takaddama ta barke tsakanin bangarorin biyu, bayan da Sanata Misau ya zargi rundunar ‘yan sandan da karbar na goro kafin yi wa wasu daga cikin jami’anta karin girma tare da handame makudan kudade daga manyan kamfanonin man fetir.

Sanata Hamman Misau ya zargi Babban Jami’in ‘Yan Sandan, Ibrahim Kpotun Idris bisa tattara kimanin naira biliyan 120 don biyan kudin tsaro. Inda ya ce irin wannan aikin tsaro ne da ake yi wa kamfanoni, bankuna da kamfanonin man fetur da mutane da yawa a kowace shekara a duk fadin kasar, amma maimakon kudin su shiga aljihun gwamnati don karin kudin shiga, sai shugaban ‘yan sandan ya azurta kansa.

Ya kuma kara da cewa hatta canjin aiki da ake yi wa kwamishinonin ‘yan sanda da manyan kwamandojin mobayel, sai sun bada cin hanci sannan za ayi masu, kuma ba kananan kudi aka karba ba, kudi ne daga naira miliyan 10 zuwa 15.

Da farko dai sanatan ya yi ikirarin cewa a matsayinsa na tsohon jami’in rundunar ya samu korafe-korafe daga manya da kananan jami’an ‘yan sanda wadanda suka yi zargin cewa sai mai uwa a gindin murhu ko kuwa wanda aljihunsa ke cike da naira ake yi wa karin girma, inda ya bayyana cewa ana karbar kimanin naira miliyoyin kudi a wurin jami’an ‘yan sanda da ke bukatar karin girman.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Tsakanin Nnamdi Kanu Da Sojojin Nijeriya: Kar A Bari Ungulu Ta Koma Gidanta Na Tsamiya (1)

Next Post

A Bi Zancen Koriya Ta Arewa Da Sannu -Putin

RelatedPosts

Kawuna

Kawuna Ya Turo Ni Kano Don Yin Garkuwa Da Mutane, In Ji Maryam  

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Maryam Muhammad, wadda ta shahara wajen...

Beli

Ka Sake Ba Ni Beli – Maina Ga Alkali

by Muhammad
2 days ago
0

Ya Ce, Da Gaske Ba Shi Da Lafiya Daga Khalid...

Bude Makarantu

Korona: Ba Ja Baya Ga Bude Makarantu – Gwamnatin Bauchi

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta...

Next Post

A Bi Zancen Koriya Ta Arewa Da Sannu -Putin

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version