Connect with us

RAHOTANNI

Sanata Rafi’u Ya Bayar Wa Daliban 21 Tallafin Karatu A Kwara

Published

on

Dalibai ashirin da daya, ‘yan asalin Kudancin jihar Kwara da suke karatu a jami’o’i daban-daban sun samu tallafin dubu dari-dari ga kowannensu daga hanun Sanata Rafi’u Ibrahim domin su samu kwarin guiwar kyautata karatunsu.
Sanatan ya zakolo dalibai uku-uku daga kananan hukumomi bakwai da suke mazabar Sanatan Kwara ta Kudu da suka kunshi Ifelodun, Offa, Oyun, Irepodun, Isin Oke-Ero hadi da Ekiti.
Dukkanin daliban sun amshi tallafin karatun ne a karkashin gidauniyar tallafi ta Sanatan mai suna, ‘Rafiu Ibrahim Bilal (RIB) Foundation’, Rafiu dai shine Sanatan da ke wakiltar mazabar Kwara ta Kudu a majalisar dattawa ta kasar Nijeriya.
Da yake jawabi a wajen mika cikicin kudin ga wadanda suka ci gajiyar a Illorin, tsohon shugaban majalisar dokokin jihar, Babatunde Mohammed, ya misalta tallafin kudaden a matsayin wata gagarumar hanyar taimakon jama’a, yana mai jinjina ga kokarin Sanatan a bisa wannan agajin tasa.
Mohammed, ya bukaci daliban da suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da su wajen samun nasarar karatunsu, yana mai jan hankulansu da kada su yi wasu ababen dab a na karatun bad a kudaden domin cimma manufar da aka basu tallafin dominsa.
A tasa jawabin, mambar kwamitin amintattu na gidauniyar RIB, Farfesa Kenneth Adeyemi, ya bayyana cewar wannan tallafi wata garabasa ce ga wadanda suka samu zarafin cin gajiyarta, yana mai jan hankulansu da kada su yi wasu ababen da kudaden ba hidimar karatu ba.
Wasu daga cikin daliban sun gode wa tallafin da Sanatan ya basu, suna masu shan alwashin yin amfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace domin kyautata iliminsu.
Advertisement

labarai