Daga Idris Aliyu Daudawa,
Jagoran jam’iyyar babbar jam’iyya mai mulkin kasa (APC, Sanata Bola Tinubu, ya yi kira da al’umma Nijeriya da cewar su zauna lafiya,a a tsakanin dukkanin kabilu,kuma addinai tunda ai duk Nijeriya daya ce.
Mista Tinubu ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a, lokacin Sallar Fidau ta kwana takwas ga marigayi Lateef Jakande, tsohon gwamnan farar hula na farko a Jihar Legas.
Ya ce kasar na fuskantar rikici amma duk ana bukatar a zauna lafiya da kuma zaman lumana.
Ya cigaba da bayanin cewa”Ina kira, a cikin tunawa da shi a yau, da kar mu sauya duk wani kalubalen da muke fuskanta a yanzu zuwa rikicin kabilanci, kabilanci da na addini.
”Idan akwai rikici, ina za mu? Za mu nutsar da Afirka ta Yamma gaba daya, ba za a sami isasshen sarari da zai saukar da mu ba.
”Wadanda suka ga yadda shi yaki yake kasancewa, tasirin rikicin kabilanci, ko rikicin addini, ba za su taba son hakan bay a faru ga Nijeriya ba.
“Muna rokon Allah ya karfafa mana hankali, ya shiryar da imaninmu, ya kuma sa akwai fahimtar juna wadda da hakan, za a iya samun abinda zai kawo zaman lafiya a wannan k tamu Nijeriya. Allah ya albarkaci dukkaninmu amin cewar Sanata Ahmed Tinubu.
Ya ce Malaman suna da matukar muhimmanci a halin da ake ciki, inda suka bukace su da addu’oi, sadaukarwa, azumi, duk wa’azin da aka shirya kan zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
”A yau,ga shi ya kasance baya tare da mu, amma har kuma mu ba zamu taba mantawa da shi ba, yana nan tare damu har abada, muna rokon jihar Legas, muna rokon Nijeriya su yi addu’a Allah ya jikas sa, ya kuma bamu dorewar zaman lafiya, da karuwar arziki, da kuma cigaba da bamu shugabanni nagari masu hankali, masu gaskiya, da rikon amana, wadanda al’ummar duniya take masu kallon mutuntawa kamar dai yadda ya yi bayani.”