Sanatan Da Ya Ci Zarafin Wata Mata Ya Nemi Afuwa

Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Sanata Elisha Abbo a ranar Laraba ya nemi afuwar matar da ya ci wa zarafi. A lokacin da sanatan yake ganawa da manema labarai a Abuja, cikin kuka ta nemi afuwar iyaye mata, ‘yan Nigeriya, ‘yan jam’iyyar sa ta PDP, majalisar dattijai, matar da ya ci wa zarafi da ‘yan uwanta da dukkan mutanan da ya baiwa kunya bisa abun da ya aikata.
Ya ce, bai taba aikata abu makamancin wannan ba a baya. Ya ce duk da abun da ya faru a tsakanin su, har zuciya ta debe shi ya ci zarafin ta, ya ce ayi hakuri, ya kuma roki maza da mata su yafe masa.
Abbo ya ce, ‘ban zo nan na fadi nawa labarin akan abun da faru ba. Nayi nadama kuma ya zama wajibi a kai na bada hakuri. Saboda haka, ni Sanata Ishaku Abbo ina baiwa duk ‘yan Nijeriya, majalisa dattawa, jam’iyyar PDP, yan uwa da abokai da duk iyaye mata hakuri. Ina baiwa Bibra da ‘yan uwan ta hakuri bisa cin zarafin ta da nayi.
Ya kara da cewa, ‘ban taba aikita abun makamancin wannan ba a baya. Ina bai bata hakuri kuma ina rokon dukkan maza da mata masu kyakkyawar zuciya su yafe min. Ajizanci ne na dan adam,’ inji shi.
Exit mobile version