Connect with us

RIGAR 'YANCI

Sanatan Filato Ta Kudu: APC Za Ta Yi Adalci – Ustaz Barikin Ladi

Published

on

USTAZ ALHAJI IBRAHIM BARIKIN LADI, SARKIN MALAMAI, shi ne sakataren kudi na jam’iyyar APC reshen Jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da Wakilin LEADERSHIP A YAU, ISAH AHMED, ya bayyana cewa, babu wanda ya isa ya yi masu kama karya. A zaben fidda gwani na tsayar da dan takarar jam’iyyar APC, a zaben cike gurbi na kujerar Sanata, da za a gudanar mazabar Filato ta kudu. Har ila yau ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne maganganun da mutane ke yi cewa, akwai sabani tsakanin Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, da Ministar Harkokin Mata, Misis Pauline Tallen. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

A matsayinka na jigo a jam’iyyar APC maye zaka ce kan zargin aka yiwa gwamnatinku ta Filato, na kasa tallafawa tallawa al’ummar jihar a wannan lokaci, na cutar annobar Kurona?
Wannan magana ba gaskiya bace, domin ni din nan ina mai tabbatar maka sheda ce, haka sauran al’umma ma sheda ce, cewa gwamnatin Filato ta tallafawa al’ummar jihar nan, a wannan lokaci na annobar Kurona. Sai dai muce idan danbu ya yi yawa, baya jin mai. Amma daidai gwargwado, gwamnatin Filato ta tallafawa al’ummar jihar nan, tun daga matakan kananan hukumomi zuwa mazabu, har ya zuwa akwatunan zabe. An bi an zabi mutane da suke da bukata, an tallafa masu da kayan abinci.

Ana zargin gwamna Lalong da niyar yin kama karya, ta hanyar tsayar da wanda yake so, a jam’iyyarku a zaben Sanata, na cike gurbi da za a gudanar a yankin Filato ta kudu, maye zaka ce kan wannan zargi?
Mu dama taken jam’iyyarmu, shi ne adalci. Don haka a matsayinmu na iyayen wannan jam’iyya ta APC, ba zamu bari ayi mana kama karya ba. Domin duk wanda yake cikin wannan jam’iyya, mu iyayensa ne. Sai da muka kafa wannan jam’iyya tayi kyau ta zama abar sha’awa, sannan kowa ya zo ya nemi takara mu ka ba shi. Gwamna Lalong bashi da mukamin komai a cikin wannan jam’iyya. Ya shigo ne ya nemi takara muka bashi, jama’a suka fito suka zabe shi, a matsayin gwamnan jihar nan karkashin wannan jam’iyya. Don haka mu da kanmu muka kafa wannan jam’iyya, saboda haka ba zamu yarda wani yazo ya yi mana kama karya ba. Domin mune shugabanni a wannan jam’iyya, don haka dole ne kowa ya yi mana da’a da biyayya a wannan jam’iyya. Saboda haka idan kaji an yi kama karya, a wannan zaben fidda gwani da za a gudanar, ba gwamna ne zai yi ba, sai dai idan mune zamu yi. Kuma mu ba zamu yi ba, domin taken jam’iyyarmu shi ne adalci. Don haka gwamna bai isa ya yi mana kamar karya ba. Idan yau ya ce zai yi mana, zamu taka masa burki. Ba zamu yarda ba, kuma ba zamu baiwa wani kofa ya yi mana haka ba. Idan gwamna ya fito ya ce yana son wannan mukami, wani ma ya fito ya ce yana son wannan mukami, kofa a bude take zamu bashi dama, domin zamu dubi cancanta ne. Don haka wannan magana ta kama karya, ba gaskiya bace.

To me za ka ce kan abubuwan da suke faruwa tsakanin gwamna Lalong da ministar harkokin mata Misis Pauline Tallen?
Duk wanda zaka ji yace yana bangaren gwamna Lalong ne, ko yana bangaren Pauline Tallen ne yana fadin ra’ayinsa ne kawai, domin a jam’iyya kowa yana da ra’ayinsa. Amma idan muka koma gida ai Pauline Tallen, uwa ce ga gwamna Lalong, don haka duk yadda zaka yi, ka raba su ba zai yiwu ba. Saboda haka duk masu cewa akwai sabani tsakanin wadannan mutane suna fada ne kawai. Amma gaskiyar magana babu wata matsala, tsakanin wadannan mutane.

To, me za ka ce kan rikicin da ke faruwa, a jam’iyyar adawa ta PDP reshen Filato?
Ka san wannan jam’iyya ta PDP babu adalci a cikin ta. Ita tana gadara da karfin mulki da kama karya ne kawai. Ayi kama karya a nuna karfi, ayi abin da ake so ayi. Don haka muke basu shawarar su dawo jam’iyyar APC mai adalci, domin ayi masu adalci. Domin duk jam’iyyr da ta tsaya kan adalci, zata cimma nasara. Rashin gaskiya da adalci ne yasa jam’iyyar PDP ta shiga cikin wannan rudani.

Ganin irin koke koken da jama’a suke yi, kan yadda kuke tafiyar da mulki, kana ganin zaku iya samun nasara, a zaben shekara ta 2023?
Wato abin da yake faruwa, idan ka duba duniya ce gabaki daya ta shiga cikin wani mawuyacin hali. Abin ya shafi kowa da kowa ne. Domin idan mutum ya dubi yadda yake sarrafa gidansa ada, yanzu idan bai tashi tsaye ba, ba zai iya yi ba. Bare mulki irin na jama’a. Mu dai muna kokari mu hado kan jama’a, don mu fuskanci wannan annoba da ta addabi duniya baki daya. Kuma abin da nake son a lura, shi ne duk adawar da ake yi kan abubuwan da suke faruwa musamman gwamnatinmu ta Filato, ba jam’iyya aka zaba ba, an zabi cancanta ne. Don haka a nan gaba ma zamu dubi, mutumin kirki mai gaskiya da adalci ne mu zaba, batare da duba jam’iyyar da ya fito ba. Don haka ina ganin babu abin da zai hana mu, samun nasara a zaben shekara ta 2023, saboda gwamnatinmu ta Filato ta taka rawa, fiye da gwamnatin da ta gabata. Domin ada muna cikin yake yake ne a jihar nan, amma yanzu muna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali da lumana. Babu shakka a yadda Filato take yanzu, mun taka rawar da gwamnatocin baya da suka gabata, basu taka ba. Saboda haka da yarda Allah, babu wata damuwa a wannan gwamnati, domin idan za ayi zabe sau goma, a jihar nan mu ne zamu yi nasara.

Wanne sako ne kake shi zuwa ga al’ummar Filato?
Sakona ga al’ummar Filato shi ne mu rungumi juna mu zauna lafiya, mu gaya wa junanmu gaskiya. Mu taru mu zabi mutumin kirki, a zabe mai zuwa na shekara ta 2023.
Advertisement

labarai