Muhammad Jamil" />

Sanatan Kebbi Ta Arewa Ya Raba Wa Manoma Injinan Ban Ruwa

Dan majalisar dattijai mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa Sanata Dr Yahaya Abdullahi ya raba Injinan ban ruwa Dari da hamsin (150) ga manonan rani a mazabar sa.

Wakilinmu ya zanta da Alhaji Ahmed Isah Gulma, daya daga cikin manoman da suka ci moriyar wannan tallafin inda ya bayyana masa da cewa irin wannan tallafin shi ne ya fi komai dadi ga manomi, saboda a wannan yanayin na noman rani ba abin da manomi ya ke bukata da ya fi a tallata masa ta bangaren noman rani.

Ya kuma yi kira ga yan siyasa da su yi koyi da maigirma Sanata Dr Yahaya musamman ta bangaren tallafawa al’umma, wanda a duk lokacin da zai yi wani abu to ya fi son ya yi shi ta inda zai yi amfani kuma zai bi duk hanyar da zai bi don ganin sakon ya isa hannun da ya kamata.

Ya kuma yi fatar Allah ya yawaita ire-iren sa wadanda ba su da ra’ayin rub da ciki kan dukiyar al’umma.

Tun farko da ya ke bayani, mataimaki na musamman kan yada labarai Malam Jamilu Gulma ya bayyana wa Wakili mu da cewa  wadannan kayan ba su ne na farko ba kuma ba su ne na karshe ba. Ya cigaba da cewa maigirma Sanata tuni ya raba daruruwan Injinan nika, kekunan dinki, KEKE NAPEP, Firjin, magunguna da kayan aikin asibiti, motoci da dai sauran kayayyakin sana’o’i ga al’ummar mazabar gundumar Kebbi ta Arewa a cikin shirin sa na yaki da zaman banza.

Ya kuma yi kira ga al’umma da a su kasance masu yi wa wannan kasar addu’ar samun cigaba da zaman Lafiya mai dorewa da kuma su cigaba da kare kafafuwan su wajen tabbatar da goyon bayan su ga shugaba Buhari.

Exit mobile version