Sani Sidi: Shekaru 51 Masu Albarka   

Daga Ahmad Maiyaki

Mutanen da suka san Muhammad Sani Sidi ba su yi mamaki ba, lokacin da  suka ji an nada shi matsayin shugaban Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa wato, NEMA, musamman wadanda suka san shi lokacin da yake Kwamishina a ma’aikatar Ayyuka da sufiri da ta Muhalla da kuma ma’aikatar Lafiya ta jihar Kaduna karkashin milkin Muhammad Namadi Sambo, da kuma lokacin Patrick Ibrahim Yakowa, wanda ya rike ma’aikatar Fasaha da al’adu, sun tabbatar cewa, ba zai ba mara da kunya ba.

An haifi Muhammad Sani Sidi ranar 12 ga Agusta, 1966. Mutum ne da yake da siyasar tafi da jama’a da tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen gudanar da aikinsa. Hakan ta dada fito wa fili lokacin da ya rike Hukumar bayar da  agajin gaggawa ta kasa na tsawon shekara daya da rabi, wanda ya mayar da Hukumar ta yi fice a Afirka.

A lokacin Muhammad Sani Sidi, ya kulla dangantaka tsakanin Hukumar da wadansu kasashen duniya, wanda hakan ya kara mata mutunci a idon duniya. Haka kuma ya kara fadada ayyukan Hukumar yadda ta dinga tafiya kafada-da-kafada tsakaninta da sauran takwarorinta na duniya.

Muhammad Sani Sidi ya yi  amfani da kwarewarsa wajen samun abokan hulda da shawarwarin da suka taimaka wa Hukumar ta zama zakaran gwajin dafi a kasshen Afirka na kudu da sahara.

Wani babban abin alfahari, shi ne, a lokacin Sani Sidi ne  aka samar da ofishin Hukumar a garin Adamawa da Ado Ekiti da Gombe da Imo da Kano da Neja da Sakkwato wadanda suka ci gaba da gudanar da ayyukansu da  sauran ofisoshin shiyyar  Hukumar da ke  dukkan shiyyar siyasa a fadin kasar nan.

Haka kuma, an kulla hulda tsakanin Hukumar da jihohi  talatin da daya da Abuja,  har ma da wadansu jami’o’in Najeriya guda shida, wadanda ke horas da jami’an Hukumar, wanda kafin zuwansa ba a samu irin wannan dama ba.

A karkashin Sani Sidi ne Hukumar ta samu nasarar tsugunar da al’ummar  da ambaliayr ruwa na shekara ta 2012, da wadanda harin ‘yan ta’adda ya daidaita, musamman mata da kananan yara, da ba su gagarumar gudummawar da ta saukaka musu rayuwa.

 

Exit mobile version