Farfesa Sani Lawan Malufashi, daya daga cikin jerin shugabanin da suka taba rike shugabancin hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano (KANSEIC) kuma na hannun daman tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce, sanin aikin hukumar zabe da kuma sirrin da yake da shi ne babban dalilin da ya sa ya bijire wa umarnin tsohon gwamnan, wanda shi ne ya nada shi shugabancin hukumar, a lokacin da aka dage zaben kananan hukumomi a Mayun shekarar 2014, wanda jam`iyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 44 da kansaloli 484.
A wannan lokacin, Farfesa Malumfashi, wanda har yanzu na hannun damar Kwankwaso ne, ya bayyana haka ne a safiyar Talata nan yayin da ya ke hira kai-tsaye da wata kafar yada labarai mai zaman kanta a Kano.
Farfesa Sani Malufashi ya ce, “ni abinda na sani shi ne, ita hukumar zabe zaman kanta ta ke yi. Don haka ban yarda wani dan siyasa ya yi min katsalandan ba. Wannan ne ma ya sa na bijire wa umarnin da Dakta Rabiu Kwankwaso ya ba ni na dage zaben da aka sa a wannan lokaci, saboda dalilan tsaro, kuma umarnin ya zo ne a ranar Juma’a, ana gobe zabe.
“A lokacin da Sakataran Gwamnati na wannan lokacin Rabiu Sulaiman Bichi, ya same ni da maganar, sai Mai Girma Gwamna Kwankwaso ya kira ni ya ce a dage zabe. Na ce, me ya sa zan dage zabe? Sai Gwamna ya ce, saboda dalilan tsaro. Sai na ce, ba zan dage ba! Ya ce, me ya sa ba za ka dage ba? Na ce, ma sa idan don maganar tsaro ne, matsalar da za a samu idan an dage zabe, ta fi wacce za a samu idan an yi zabe.
Haka kuma Farfesa, ya kara da cewa ita harkar zabe tana bukatar kudi masu yawa ya ce wani sirri kuma da ya sa na yi nasara shi ne kasancewa ta Baare wato mutumin Arewa sai na dabo manyan Malamai wanda na yarda da su nagari na cikin NIjeriya da na NIjer makotanmu na sa su addu
a kwana 40 ana rukon Allah kafin lokacin zabe don a yi lafiya wasu suna zau ne a wani wuri a hukumar zabe wasu kuma na kai su wani wuri su ma suna addu`a, to wannan ina ganin shi ne sirrin yin nasarar zaben kananan hukumomi na 2014 lafiya a Kano, domin ina da labarin an ce wasu na shigo da makamai don kai hare-hare a lokacin zaben tun da a lokacin ana rikicin Boko Haram Allah dai ya kiyaye aka yi lafiya.
Sai kuma batun cewa shi ne karo na farko da Jam`iyya daya ta cinye zaben na Kano wato APC to ko bayan kammala zaben sai da na gaya wa Dakta Rabiu Musa Kwankwaso cewa ka rubuta ka ajiye, zaben kasa ma mai zuwa 2015 APC ce za ta cinye gaba daya kamar yadda aka yi wannan zabe na kananan hukumomi. Haka kuma aka yi APC ta lashe Sanatoci Uku na Kano ‘Yan Majalisar Tarayya 24 ‘Yan Majalisar Jiha 40 duk APC ce, ya cinye a zaben 2015 wanda aka zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015, kuma banbanci yawan kuri’ar da aka kada a zaben kananan hukumomin Kano da na gabatar a 2014 da kuma zaben da hukumar INEC ta gabatar a 2015 na kasa a Kano banbancin kuri’a 200 ne kacal suka fi a kananan hukumomi da aka kada a wancan lokacin.
Har’ila yau da zabe ya kusa zuwa ya rage ‘yan kwanaki kamar hudu na fadawa ma’ikatana na KANCEK cewa, kowa ya kwaso kayansa ya tare a ofis a nan muka zauna kowa da kayan wankansa da suturarsa ta sawa muka tare a hukumar muna aiki ba dare ba rana, kwana uku cir ban yi barci ba.
Tun da farko sai da ya bayyana cewa babbar nasarar da ya samu a kowane zabe a duniya shi ne wayar da kan masu zabe da cusa musu ilimi da muhinmancin yin zabe ko kada kuri`a da wanda suke so su zaba, wannan shi ne baban jigon samun nasarar zabe da na yi don haka ina tausaya wa Farfesa Sheka a wannan zabe.