Ibrahim Muhammad" />

Sanya Sunan Malama Zahra’u A Wadanda Za’ A Yi Wa Kwamishina A Kano Ya Yi Daidai, inji Uwa Matar Xansanda

‘Yar siyasa kuma tsohuwar mataimakiya ta musamman ga Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar  Ganduje a ma’aikatar al’amuran Mata, Hajiya Uwa Matar Dansanda ta bayyana cewa, Hajiya Dakta Zahra’u Muhammad babbar Kwamandar Mata ta Hisbah ta cancanci zabin da Gwamna ya yi mata don tantanceta a sahun wadanda za’a nada a mukamin  kwamishina a jihar Kano.

Ta yi nuni da cewa Dakta Zahra’u, jajirtacciyace mai kwazo da tausayi ga rikon amana, Mace ce da take kauna ga Gwamna da iyalansa take son ganin nasararsu  ta bada gudummuwa sosai domin tabbatar da nasarar zaben Gwamna da aka yi, ga taimakawa ‘yan jam’iyya.

Hajiya Uwa Matar Dansanda ta yi nuni da cewa Hajiya Zahra’u kowa ya santa a fagen tallafawa cigaban mata da marayu da iyayensu duk shekara sai ta yi taro cikin watan azumi ta yi musu tagomashi na alkhairi ta raba kayan abinci da sutura sannan ta bada tallafin jari, banda wanda take yi akai-akai ga daidaikun mabukata maza da mata yau da kullum.

Ta kara da cewa kullum aikin Malama Zahra’u shi ne umurni da kyakkyawa da hani da mummuna.Ta yi tafsiri da tunatarwa akan kyautata tarbiyar al’umma.

Hajiya Uwa Matar DanSanda ta yi fatan nadin da za’a yi wa Babbar Kwamandiyar Hisbar ta Mata a matsayin kwamishina ya zama karin alheri da cigaba ga matan jihar Kano da al’ummarta gaba daya.

Exit mobile version