Connect with us

LABARAI

Saraki Ya Hada Kan ‘Yan Jam’iyyar PDP A Jihar Osun

Published

on

Shugaban Majalisar Dattijai Dakta Abubaka Bukola Saraki, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamman da za a gudanar a jihar Osun na jam’iyyar adawa ta PDP, ya hada kan dukkan bangarorin jam’iyyar PDP na jihar wadanda ba sa ga maciji da juna tun bayan zaben fid da gwani da ka gudanar kwanakin baya.

Dakta Saraki ya bayyana haka ne ta shafinsa ta kafar sadarwar Twiter @BukolaSaraki, inda ya tabbatar da cewa, bangarorin guda biyu da ba sa ga maciji da juna sun rattaba hanun a kan yarjejeniyar zama lafiya tare da aiki tare don samun nasarar zabe mai zuwa.

Saraki ya kuma kara da cewa, “Bayan taro na tsawon lokaci da muka gudanar da bangarrorin guda biuyu da safen nan, ina mai farin cikin shaida maku cewa, an cimma yarjejeniya tsakanin dan takarar gwamna na jam’iyyarmu ta PDP Sanata Ademola Adeleke da kuma abokin karawarsa a zabe fid da gwani Dakta Akin Ogunbiyi, a dai dai lokacin da muke fuskastar zaben gwamna da za a gudanar a ranar 22 ga watan Satumba 2018, wannan yana nuna cewa, jam’iyyarmu na samun ci gaba yadda ya kamata.”

A wata sabuwa kuma, Shugaban Majalisar Dattijai, Dakta Bukola Saraki, ya mayar da martani a kan bayanan da jami’in watsa labarai na jam’iyyar APC, Mista Yekinni Nabena, ya yi a kansa.

Shugaban Majalisar Datijai Bukola Saraki, ya mayar da martanin ne ta hannu mai ba shi shawara a kan harkokin watsa labarai, Mista Yusuph Olaniyonu, a takardar da ya raba wa manema labarai a Abuja jiya, ya kara da cewa, soki burutsun dake fitowa daga bangaren jam’iyyar APC ba za su rudar da shi ba daga gudanar da aiyyukansa na ci gaban al’umma. Ya kuma ce, bangeran Saraki a shirye suke don tattaunawar gaba da gaba da Mista Yekinni Nabena a kowanne gidan talabijin na kasar nan a kan dukkan abin da ya ke korafi a kai, ya kuma kamata ya fito fili don jama’a su san shi ba wai ya ringa boyewa ba, yana raba takardun da aka rubuta masa daga Legas.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: