Bello Hamza" />

Saraki Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Sarkin ‘Etsu Patigi’

Shugaban majalisar dattijai, dakta Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana kaduwarsa a bisa rasuwa daya daga ciukin shaharraren sarakuna gargajiyan jihar Kwara, Etsu na Patigi, Alhaji Umar Chatta Ibrahim.
Sanata Saraki ya bayyana haka ne a sanarwar da ta fito ta hannun jami’in watsa labaransa, Mista Yusuph Olaniyonu, y ace, a zamanin mulkin magayyin an samu cikakken zaman lafaya da ci gaba a jhar Kwara da ma Nijeriiya baki daya.
“Alhaji Umar Chatta Ibrahim dattijo ne kuma magoya baya na ne, ina daukarsa a matsatyin mahaifi, lallai zan yi asarar shwarwarinsa na mahaifi, da kuma dangantakarsa tsakanin dukkan bangarorin al’ummar jihar Kwara, kuma zamu yi kewansa kwarar da gaske.
“na yi masa ganin karshe ne a lokacn yakin neman zabe, yana da cikakkne fata na gari ga al’ummar garin Patigi, musamman kuma ga al’ummar mazabar majalisar dattijai ta Kwara ta tsakiya, yana kuma matukar kokarin ganin an samar wa al’ummar yankinsa dukkan c/ gaban daya kamata, ban taba tunanin wannnan haduwar ne na karshe a tsakaninmu ba”, inji Saraki.
Shugaban majalisar dattijai na mika ta’aziyyarsa ga iyalai da al’ummar masarautar Patigi da majalisar sarakuna Patigi da majalisar Sarakuna jihar Kwara gaba daya da kuma al’ummar jihar Kwara a bisa wannan babban rashin da muka yi.

Exit mobile version