Connect with us

LABARAI

Saraki Zai Jagoranci PDP A Zaben Gwamnan Jihar Osun

Published

on

Jam’iyyar PDP ta nada Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, a matsayin jagoran tawagar kusoshin Jam’iyyar 85 da za su jagoranci kamfen din neman gwamnan Jihar Osun a zaben gwamnan Jihar da za a yi a ranar 22 ga watan Satumba.

Hakanan, Jam’iyyar ta PDP ta kwatanta Jam’iyyar APC a matsayin, Shekar barayin kasar nan.

Da yake magana, Saraki ya bukaci Shugaba Buhari da ya tsayu a kan alkawarin da ya dauka na gudanar da zabe na gaskiya, ya bayar da misalin hakan a zaben na Jihar ta Osun.

Saraki ya ce, baya ga shaharar da dan takarar na Jam’iyyar PDP a Jihar ta Osun yake da shi, al’umman Jihar ma sun nu na bukatar su ta neman canji a Jihar.

Saraki ya ce, daukakar ta Jam’iyyar APC ya dushe a Jihar ta Osun, sakamakon zargin rashin iya shugabancin Jam’iyyar ta APC a Jihar ta Osun.

Ya ce, bai kamata PDP ta fadi a zaben na Jihar Osun ba, kasantuwan ta fadi a baya a zabukan Jihohin Ondo da Ekiti.

“Ya zama tilas mu ci Jihar Osun, domin mu tabbatar wa duniya, Osun gidan Jam’iyyar PDP ce.

Saraki ya yi kira ga shugabannin na Jam’iyyar PDP, da su ci gajiyar rarrabuwar da ke tsakanin ‘ya’yan Jam’iyyar ta APC su lashe zaben Jihar.
Advertisement

labarai