Sarakuna Da Malaman Addini Na Da Matukar Muhimmanci Wajen Gina Kasa – Gwamnan Neja    

Addini

Daga Muhammad Awwal Umar,

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa akwai bukatar sarakunan gargajiya da malaman addini su rika taka rawa wajen samar da ingantaccen tsaro a kasar nan, domin suna da matukar muhimmanci wajen gina kasa.

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a taron bikin nadin sarautar Mai Martaba Oba Repheal Ajibola Olaleye Oluyede, Ise Oluwa II kuma Alayede na Ogbese na Jihar Ondo.

 

Gwamnan ya bayyana cewa sarakunan gargajiya da malaman addini suna da rawar takawa a cikin al’umma wajen fuskantar matsalolin da kasar nan ke ciki musamman rashin tsaro da ya yi katutu a wasu sassan kasar nan.

 

Gwamnan ya bayyana sabon basaraken a matsayin mai riko da addini da kuma jigo wajen gwagwarmayar kare hakkin Dan’adam, inda ya bayyana cewa mutanen Ogbese ta Jihar Ondo ba za su yi nadamar zaben basaraken ba.

 

“Na na san shi sosai, mutum ne mai jama’a, zan ba ku tabbacin cewe zai kawo ci gaba a masarautar nan.

 

“Ina kyautata zaton al’ummar Alayede Ogbese zai ci gaba da bunkasa a karkashin ikon sa.”

 

A bayanin sabon basaraken, Mai Martaba Oba Olaleye Oluyede ya yaba wa Gwamna Abubakar Sani Bello da ya samu damar halartar bikin nadin sarautarsa, wanda ya yi daidai da shekaru arba’in da aurensa.

 

Oban yana daya daga cikin daraktocin farko na kamfanin Mainstream Energy Solution Limited da ke Jihar Neja, lauya ne kuma babban malamin addinin Kirista

Exit mobile version