Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya gana da Sarakunan Gargajiya da shugabannin gundumomi daga sassa daban-daban na jihar, da nufin neman gudumawar su gurin yaki da yaduwar annobar cutar Korona a jihar, da kuma taimaka musu kan yadda za a magance matsalolin tsaro da ke addabar al’umman jihar musamman ‘yan fashi da masu satar mutane domin neman kudin fansa.
A cewar Gwamnan, taron wanda ya kasance a matsayin misali na gwamnatin jihar, zai kuma ba wa gwamnatinsa damar yin saka tare da shugabannin gundumomi don ci gaba da wayar da kan da ake bukata game da annobar cutar.
Ya ce sarakunan gargajiya hakimai da dakatai sun fi kusa da al’umma saboda haka duk wata hanya ta samar da tsaro sai an yi amfani da sanya hannunsu domin tabbatar dasamun nasarar tsaro cikin jihar.
Da yake tsokaci game da yaduwar kwayar cutar, gwamnan ya yi gargadin cewa har yanzu cutar na yaduwa, don haka yana mai kira ga hakiman yankin da cewa ba wai kawai su nuna damuwar gwamnati a kan batun ba, ana bukatar taimakawarsu.