Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Sarakunan Gargajiya Sun Kai Wa Shugaban Kasa Ziyara Fadar Aso Villa

Sarakunan gargajiyar kasar nan sun kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.
Rahotanni sun bayyana cewa Sarakunan sun kai wa shugaban kasa ziyarar ne ta jinjina da ban girma tare da taya shi murnar sake lashe zaben shugaban kasa karo na biyu, a zaben da aka yi ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu.
Ooni na Ife, Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya roki shugaban kasa da ya ja abokan hamayya sa a jiki kuma kada ya saurari sukar da suke masa, Wasu daga cikin sarakunan da suka halarci zaman sun hada da da sarkin Zaria, Alhaji Dakta Shehu Idris, Amayanabo na Twon Brass, sarki Alfred Diete-Spiff; sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Bashar, Attah na Igala, Idakwo Micheal Ameh; Gbong Gwom din Jos, Jacob Gyang Buba;  sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari, sai kuma Sheikh Isah Ali Pantami da sauran manyan Sarakuna daga yankin kudancin kasar nan.
A wani labarin kuma, Mai alfarma Sarkin Musulmi, kuma shugaban kungiyar Jama’til Nasaril Islam, Alhaji Sa’adu Abubakar III ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar samun nasara a zaben 2019 daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.
Har ila yau, Sarkin Musulmai yayi kira ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, daya rungumi kaddara, ya saduda, don a samu zaman lafiya, Sultan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kungiyar JNI ta fitar a ranar Lahadi a babban ofishinta dake garin Kaduna ta bakin babban sakataren hukumar, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, inda yace JNI na godiya ga Allah daya tabbatar da zaman lafiya a zaben daya gabata
Exit mobile version