Connect with us

TARIHI

Sarautar Sarkin Musulmi Da Gwagwarmayar Rikon Sarauta (5)

Published

on

Cigaba daga makon jiya.

4. Sarautar Sarkin Musulmi Ahmadu Dan Atiku

Kwanaki uku da rasuwar sarkin Musulmi Aliyu sai aka yiwa Ahmadu ɗan Abubakar Atiku ɗan shehu Usmanu mubaya’ar sarauta. Yayi alkawari da tsayar da gaskiya da adalci, ya hori mutane da abubuwa huɗu: na ɗaya su bar sayar da gonaki, na biyu subar amsar gunki, na uku su amsa kiran alkalai, na huɗu su amsa kiransa idan ya nemesu tafiya izuwa yakin jihadi.

Akwai daga yake-yakensa yakin Karaziru, da Yakin Sauwa, da yakin ruwan Bore, da yakin Gumi. Shi ne sarkin daya rayar da Cimmola, ya gina birni acikinta, da masallatai har ake sallar jumu’a a ciki.

Kuma a acikin wannan gari Cimmola ya rasu bayan yayi shekaru bakwai da wata biyu da kwana 26 yana sarauta, yana da shekaru 60 da haihuwa.

Da fatan Allah ya rahamsheshi Amin.

5. Sarautar Sarkin Musulmi Aliyu Na Biyu

Shi ne Aliyu ɗan sarkin Musulmi Muhammadu Bello, kuma shi ya kasan ce ɗan uwan Sarkin Musulmi Aliyu na farko ne.

An yi ma sa mubaya’ar mulki a Chimmola bayan kwanaki huɗu da rasuwar Sarkin Musulmi Ahmadu ɗan Abubakar Atiku.

Daga nan sai ya taso izuwa Wurno da zama, shine na shidda da sarautar sarkin Musulmi idan aka soma lissafi da shehu Usmanu, amma na biyar daga Muhammdu ƁBello.

Ya yi watanni goma sha ɗaya da kwanaki 19 bisa sarauta ya rasu yana da shekaru 60 da haihuwa. Kabarinsa na nan a wurno kusa dana mahaifinsa.

Da fatan Allah ya jikansa Amin.

6. Sarautar Sarkin Musulmi Ahmadu Rufai Dan Shehu Usmanu

Kwanaki biyar da rasuwar sarkin Musulmi Aliyu, sai akayiwa Ahmadu Rufa’i ɗan shehu Usmanu mubaya’ar mulki a masallacin wurno.

Bai jima awurno ba ya komo Sokoto da zama, ya gyara masallatai da gina sababbi, ya rayar da garin sosai, kullum kuma yana cikinsa har ma ana cewa aduk tsawon zamanin sarautar sa kimanin shekaru biyar bai fita daga Sokoto ba sai sau uku kacal.

Na farko domin tafiya ginin birnin Silame. Na biyu domin korar kafirrai daga Kware sanda suka sauka a wata alkarya mai suna kayama. Na uku ya kara fita zuwa Kware domin ta’aziyyar ɗan uwansa Mallam Isa ɗan shehu Usmanu bin fodio.

A zamaninsa, an samu zama lafiya da kwanciyar hankali a daular Musulunci. Shi ne sarkin daya soma yanke hannuwan ‘yamfashi idan an kamo su tun bayan rasuwar Shehu Usmanu.

Ya rasu yana da shekaru 61, bayan ya shafe shekaru 5 da watanni 6 da kwanaki 20 bisa sarauta. Kabarinsa na Sokoto shima.

Da fatan Allah ya jikansa amin.

7. Sarautar Sarkin Musulmi Abubakar Na Biyu, Mai Rabah Dan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello

Daga nan kuma sai aka yiwa Abubakar mubaya’ar sarauta a Sokoto. A zamaninsa anyi yake-yake a kalla guda uku. Su ne:- Yakin gidan karari, da yakin Farintau da yakin Madarumfa.

Wannan sarki ya zamo mai tsoron Allah da kamanta adalci ga mabiya, ya rasu a Wurno yana da shekaru 63 da haihuwa. Kabarinsa na nan kusa da na mahaifinsa, Muhammadu Bello, a Wurno.

Da fatan Allah ya ji kan sa, amin.

8. Sarautar Sarkin Musulmi Mu’azu Dan Muhammadu Bello

Daga nan sai akayiwa Jikan shehu na karshe a jerin sarakunan Musulunci sarauta, watau Mu’azu ɗan muhammadu Bello a wurno.

A lokacinsa yayi yaki mai tsanani da Sabon Birni, amma bai samu nasarar cinyeta ba kuma yayi kokarin samar da zama lafiya ga masarautarsa.

A karshe ya rasu yana da shekaru 68 da haihuwa bayan ya cika shekaru 4 da watanni 9 yana mulki. Kabarinsa yana nan a Sokoto kusa da hubbalen shehu.

Allah ya ji kan sa, amin

9. Sarautar Sarkin Musulmi Ummaru Dan Aliyu Dan Muhammadu Bello

Daga nan sai akayiwa Ummaru mubaya’a nan cikin masallaci Bello a Sokoto. A yake-yakensa akwai yakin Sabon Birni, inda yaje domin ɗaukar fansar uba gareshi, marigayi sarkin Musulmi Mu’azu. Haka kuma ya kai yaki Argungu da Madarumfa.

A zamanimsa ne turawa suka yawaita shigowa kasar Sokoto, har aka gane cewa su ba sharifai bane kamar yadda a baya suke ɓoye kansu domin su samu ikon yawo cikin kasa da yin ciniki.

A waɗannan zagaye na turawa suka san kasa dukkanta, suka san koramu da garuruwan kasar Hausa, suka isa ga sarkin Musulmi suka yi cinikayya da mu’amala da shi har zuwa rasuwarsa.

A zamaninsa turawa sun ba shi agogo don sanin lokaci, da wani gado mai yin fifita da mafitai idan an zauna a kansa da gambuna masu fenti da sauransu.

Haka kuma a zamaninsa, yakan yi zama lokaci lokaci da sarakunan gabas a Kauran Namoda. Kuma a kauran Namoda ɗin ya rasu, ya na da shekarun haihuwa 69 bayan ya yi shekara 9 da watanni 10 bisa kan sarauta.

Cigaba a makon gobe da yardar Allah.
Advertisement

labarai