Connect with us

TARIHI

Sarautar Sarkin Musulmi Da Gwagwarmayar Riqon Sarauta (3)

Published

on

Cigaba daga jiya.

 

  1. Sarautar Sarkin Musulmi Abubakar Atiku

Bayan kwana bakwai da rasuwar Muhammad Bello, sai akayiwa Abubakar Atiku mubaya’a. Shi kuwa ya kasan ce ɗane ga Shehu Usmanu ɗan fodio, watau kaniɓga Muhammadu Bello. Kuma ya kasan ce masanin sirruka.

Har ma an ce mahaifinsa ya sanar dashi sirruka 115, shikuwa sai ya sanar da 15 ga jama’a, ya bar 100 bai sanar da kowa ba.

Amma ga maison samun sirrikan daya sanar, sai ya nemi lityafin ‘Tabshirul Ikhwan’ na Abdulkadir Macciɗo Waziri.

 

Yaqe-yaqe

Bayan Sarkin Musulmi Abubakar Atiku ya hau gadon sarauta, sai kafiran amana na zamfara dana gobir suka warware alkawari, don haka sai yayi tattalin yaki, ya fuskanci Burmi.

Ya yi tafiya har ya iske birnin Damri. Ya iske sarakunan zamfara sun taru cikinsa, yayi faɗa dasu, kuma ya samu nasara.

Sannan ya ɗaura yaki ya isa karkarar Katsina, yayi sansani anan, sannan ya zabura zuwa birnin Cikaji yayi yaki dasu mai tsanani, yayi zamansa kwanaki da dama, sannan ya koma gida.

Daga can kuma ya ɗaura yaki zuwa zurmi, ya aike Abdul Hasanu ɗan sarkin yaki Aliyu Jedi, ya fita garesu da runduna, yayi faɗa dasu ya komo gida.

Sannan yayi tattalin yakin Attabu (yakin gayya) wanda ya kira sarakunan gabas ya gamu dasu acikin kasar zurmi. Ya tashi ya nufi Gobir, ya kokarta ya riski Tsibiri, ya sauka Rumka, ya iske mutanen Gobir, katsinawa, Azbinawa da mutan Borno sun taru acan.

Ya fara yaki dasu tun hantsi har la’asar. Allah ya bashi nasara ya karya su ya koma gida.

Sanna ya ɗaura yaki zuwa kasar Gummi, ya kwana 8 ya ɓata abincin karkararsu duka, suka firgita dashi, sannan ya komo ta zurmi, ya dawo gida.

Da lokacin kaka yayi, sai ya sake gayyatar sarakunan gabas, suka zo da shirin jihadi, suka fita da yaki har Zamfara, suka fuskanci Gobir.

Ya shiga cikinta yayi sansani, Ya kwana uku, sannan ya nufi tsibiri da yaki. Mutanensa suka aukawa tsibiri da yaki mai tsanani. Anan suka wanzu har kwanaki biyar.

A cikin haka sai ya lura mutane jikinsu yayi sanyi da yaki, don haka ya juyo ya tsallaka gulbi, babu wani alamun ciwo jikinsa.

Lalura ta sameshi ranar 27 ga watan Ramalana, ya zamo ana ɗauke dashi a wuya har suka iso wani wurin da ake cewa Nasarawa cikin kasar Zamfara duka sauka. Ya kwana 18 anan, sannan ya hau zuwa Kuturu. Ranar alhamis kuwa ya rasu a nan. Don haka Kabarinsa nanan a Katuru. Da fatan Allah ya gafarta masa Amin.

Sa’ar da aka kare jana’izarsa, sai waziri Babba Abdulkadir ɗan waziri Giɗaɗo ɗan Laima yayi ban kwana da sarakunan gabas suka koma gida.

Zaɓaɓɓun da suka rasu kuwa a lokacinsa akwai ɗan uwansa Buhari, da Alkali Bi’ali, da Mustafa marubucin shehu Usmanu, da mallam ishaqa da Mallam Mani da wasunsu.

Sarkin Musulmi Abubakar Atiku ne sarki na farko daya rasu yana dawowa daga yaki.

Daga nan sarakunan Sokoto suka zaɓi Aliyu Babba ɗan Muhammadu Bello ɗan Shehu Usmanu ya zama sarkin Musulmi.

Cigaba a makon gobe in sha Allahu.

 

Ali Abubakar Sadik
Advertisement

labarai