Mustapha Ibrahim">

Sardaunan Bagadawa Ya Yaba Wa Masarautar Bichi

Alhaji Sunusi Ahmad Danbaba, sabon Sardaunan Bagadawa ya yaba wa Masaurautar Bichi bisa jagorancin Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, da Hakimin Dawakin Tofa Daillaci Bichi, Dr. Maikano Rabi’u da kuma Dagacin Bagadawa, Alhaji Galadima kan amincewarsu da yadda da nada shi Sardauna da ’yan uwansa a kan nada su, don bada gudunmawa a wannan gari na Bagadawa da ke karkashin Masaurautar Bichi da ke Jihar Kano.

Saradunan ya bayyana haka ne a bikin nadin sarautun da a ka yi a garin Bagadawa ranar Asabar da ta gabata, inda kuma ya yi alwashin cigaba da bada hadin kai da wannan masarauta ta Bichi.

Sauran wadanda a ka nada sun hada da Alhaji Ubale Musa a matsahin Santalin Bagadawa, Malam Usaini Abdulhamid a matsayin Talban Bagadawa, sai kuma Alhaji Magaji Ahmad Mahmud a matsayin sabon Sarkin Noman Bagadawa, wanda kuma dukkaninsu sun sha alwashin bada gudinmawarsu ga dagacin Bagadawa Alhaji Lawan Galadima da Masarautar Bichi bakidaya da ta amince a nada su a wadannan mukamai.

Shi ma wakilin Hakimin Dawakin Tofa, Alhaji Salusu Tsaho, ya bayyana cewa, ganin yadda wadannan nade-nade za su kawo cigaba ya sa hakimin ya amince a yi nadin.

Exit mobile version