Mustapha Ibrahim" />

Sare Bishiya Mai Hoton Ka’aba Ya Jawo Raunata ’Yan Hisbah A Kano

Sakamakon bayyanar wata bishiya a karamar hukumar Kunci da ke jahar Kano, wacce a ka gan ta da hoton Ka’aba da tauraro a jikinta ya sa ta zama abin al’ajabi ga al’umma in da wasu su ka fara neman tabarraki da yin dawafi da dai sauran nau’i na ibada da wannan bishiya. Hakan ce ta jawo wasu kauyawan su ka kewaye ta su na karbar kudi ga masu ziyartar wannan Bishiya.

Sai dai kuma ganin hakan na da hatsari ga imanin Musulmi da tauhidinsu, kamar yadda babban kwamandan hukumar Hisbah na Kano, Sheik Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana haka cewa bayan sun yi buncike sun gano wannan lamari, sai hukumar ta umarci dakarunta a kan sare wannan bishiya, wanda hakan ce ta jawo kauyawa masu karbar kudi su ka aukama ’yan hisbar da sara, inda su ka jikkata mutum hudu ta hanyar sara da kararrayawa.

Yanzu haka dai wadanda su ka yi wannan aika-aika sun ari takalman kare, amma hukumar ta Hisbah ta bazama neman su ruwa a jallo, kamar yadda Sheik Daurawa ya bayyana.

Na Shigo Harkar Adabi Lokacin Masana Hausa Na Kyamar Marubuta –Farfesa Abdalla

FARFESA ABDALLA UBA ADAMU ba ya bukatar doguwar gabatarwa ga masu bibiyar harkokin Adabin Hausa a tarayyar Nijeriya, Afrika da ma duniya bakidaya, saboda irin rawar da ya ke takawa wajen cigaban fannin da ma yadda ya rungumi matasa masu fasahar kirkira a yankin arewacin Nijeriya, musamman ma a lokacin da a ke kyamar su, kamar marubuta Litattafan Soyayya da masu matasa masu shirya finafinan Hausa. A yanzu an yi ittifakin cewa, babu masani kuma manazarci wanda ya tara muhimman bayanai kan wadannan masana’antu da matasa su ka kafawa kansu na rubutu da finafinan Hausa, kamar wannan kasurgumin farfesa.

Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya samu zarafin yin doguwar zantawa da Farfesa Adamu, domin jin sirrin yadda ya samu wannan gagarumar nasara mai cike da tarihi a kasar Hausa. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance, wacce za mu rika tsakuro mu ku ita mako-mako:

Da farko za mu so mu san tarihin rayuwarka.

An haife ni a unguwar Daneji a Kano a shekarar 1956 a ranar 25 ga watan Afrilu. Yanzu na kai shekara 62 kenan. Duk karatuna a Kano na yi su na firamare da sakandare. Firamare dai a Dandago na yi ta, na koma Tudun Madatai, sakandare kuma Gwale Sakandare na gama a 1973. To, daga nan kuma mu ka tafi CAS (Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a ta Kano). Mu ne mu ka bude CAS a watan Nuwamba 1973. Mun zauna a CAS kusan shekara uku. To, daga nan kuma mu ka shiga jami’ar Ahmadu Bello a 1976 na karanta Bsc Science Education, wato ilimin horar da malaman kimiyya; yadda malaman kimiyyar za su koyar da yara ’yan sakandare. Da na gama a 1979 na je hidimar kasa a jihar Imo, inda na koyar da Biology, wato sirrin halitta. Na yi shekara guda a nan, wato 1979 zwa 1980 na dawo Kano na samu aiki da jami’ar Bayero a matsayin malamin matakin farko, wato Graduate Assistant a Sashen Ilimi karkashin Tsangayar Ilimin jami’ar. To, daga 1980 din na dinga tafiya a hankali-a hankali har Allah Ya kai ni 1997, inda na zama farfesa.

To, ita jami’ar Bayero farkon shigarmu sun ba mu gudunmawa wajen karatu. Saboda haka a 1981 a ka tura ni Jami’ar London na yi digiri na biyu (Masters) na dawo 1983. A 1985 na sake fita na je na yi PhD (digirin-digirgir) a Jami’ar Sussed ita ma a Ingila a Science Education, na dawo a 1988 na cigaba da aikina a jami’ar Bayero. Bayan kamar shekara kamar uku ko hudu a 1991 na samu daman a tafi Amurka na je na koyar a Jami’ar California da ke Berkeley tsawon shekara guda a karkashin wani tallafin gwamnatin America. To, a nan na koyar har ma na wallafa wani littafi, wanda a ka buga shi a Amerika din. To, bayan na dawo a 1992 na cigaba da zamana a BUK din Ina koyarwa Ina bincike. A 1992 na tafi kasar Italiya Ina nazari a kan harkar ilimi. To, bayan na dawo, 1993 na cigaba da bincikena da koyarwa. A 1997 na zama farfesan kimiyya, wanda ni ne na farko da zama Professor of Science daga Kano.

To, da na zama farfesa a 1997, sai na ga a lokacin shekarata 41; Ina da ragowar shekara 24, idan Allah Ya ba mu rai kafin na yi ritaya. To, sai na ga ba ni sha’awar na zauna a fannin nazarin ilimin har tsawon shekara 24; gani na ke yin a riga na yi abinda zan yi, saboda duk abinda z aka yi a fannin nazarin ilimi a na yi a kan jarrabawar yara, ya za a yi a daukaka ilimin yara, ya za a yi a yi kaza-a yi kaza! Kuma wanda gwamnati yakamata ta yi wannan, domin a karshen binciken za ka ji an ce, gwamnati ya kamata ta yi kaza, kuma gwamnatin ta na kokari ta na yi. To, abin ne ya yi yawa. Ka san an ce, idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai. To, gwamnati ba za ta iya ba, kai kuma a matsayinka na manazarci kullum abinda ka ke tonowa kenan; yara ba sa cin jarrabawa, gwamnati kamata ya yi ta yi kaza; malamai ga dabarun da za ku koyar, malaman kuma bas a amfani da wannan dabarun, saboda idan sun yi amfani da su yaran ba cin jarrabawar za su yi ba; makarantu babu kayan karatu, babu dakin karatu, babu littafai; iyayen yara ba sa tallafa mu su, mutum ne za ka ga ya na da mata uku ’ya’ya wajen 10 kuma kowanne yaro zai zo makaranta. Saboda haka ina zai ba su kudin makaranta, ina zai bas u litattafai, ina zai ba su kaza da kaza? Saboda haka yaro idan Allah Ya ba shi karatu ya ci, idan bai ci ba, bai ci ba. Kai kuma a matsayinka na manazarci sai a ga cewa kamar babu wani takamaiman abu; gani za ka yi duk wani nazari da za a yi, bai bullewa. Sai n ace, gaskiyar magana bari na nemi wani abu wanda ni na ke da sha’awa a kai, wanda ni ba na tunanin ya kai ni ga ko’ina. Wato abinda dai zan zauna Ina bincike a kai, Ina nazari a kai har ya sa a cikin shekara 24 din nan na san inda na nufa. To, da ma can tun Ina yaro na ke da sha’awar rubutu, na ke da sha’awar fim, na ke da sha’awar kade-kade da wakoki. Amma na fi damuwa da wake-waken na Turai.

To, a dab da lokacin da na yi wannan tunanin na cewa na kauce din, sai ya zamanto marubutan Hausa a kasar Hausa su na samun kalubale. Kuma idan na ce marubuta, Ina nufin marubutan zamani, wadanda a ke kiran rubutansu da Litattadan Soyayya ko wani abu haka. Su na samun kalubale, kuma inda na fara ganin kalubalen shi ne, an tura ni na je na yi abinda a ke cewa ‘Teaching Practice Superbision’. Wato duk dalibin da zai koyar sai an kai shi makaranta ya je ya yi gwaji a wata makaranta. To, a na tura malamai su je su duba su ga yaya ya iya? Su gyara ma sa kuskurensa. To, Ina daya daga cikin wadanda a ke turawa din. Saboda haka na je aji sai nag a yaro ya na fada da wata yarinya… Na ke ji a Jogana ne… Yan a ta fada, ya kwak-kwace wasu abubuwa a hannunta, ya cigaba da karatunsa. Sai bayan da y agama darasin sai na tambaye shi, me ya faru. Sai ya dauko litattafan ya ce, ‘ka ga wadannan liattafan soyayyar, su ne masifarmu! Yara duk wadannan su ke karantawa, ba sa mayar da hankalinsu a kan karatu!’ Sai na ce, ‘ah! idan har wadannan su ke karantawa, ashe idan har wadannan su ke karantawa, akwai ‘reading culture’ kenan.’ Sai ya ce, ‘eh, sun a yi, amma ai ba wadannan yakamata su rika karantawa ba; litattafansu na manhajoji na karatu su ya kamata su rika karantawa, don su ci jarrabawa, amma ba sa karanta wadannan’. Na ce, ‘ba kwa ganin ba sa karantawa ne, saboda babu su?’ Ya ce, ‘to da wannan ma kam; babu litattafan’. Saboda haka abinda su ke da shi, shi su ke karantawa. To, a lokacin ne na fara tunanin ni wannan abin kamata ya yi mutum ya yi nazari a kan wadannan abaibadan.

Kuma lillahi wa rasulihi na yi kokarin na san su waye su ka yi nazari a kan wadannan litattafan, domin a ga an fito da wata hanya ta fahimtar abun, to sai na ga ashe an jima a na tafka mahawara a kan wadannan litattafan. Su wadanda su ka karanta ilimin Hausa, su ka yi karatu a kan ilimin Hausa, sun gama tattara wadannan litattafan nasu gabadaya sun jefa su a kwandon shara a matsayin bas u da wani amfani, bas u da wani muhimmanci. To, kuma a rediyo a wajejen 1996-1997 sai a ke yawan kalubalantar marubutan nan. Ina jin wannan a rediyo a na cewa, wadannan marubutan su ne su ke dauke hankalin yara, su ke kaza-su ke kaza har ya zamanto cewa shekara ta 2001 ma gwamnatin Kano ta riga ta haramta fitar da litattafan nan da finafinan da su ka biyo baya, saboda a na ganin su ne su ke hana yara cin jarrabawa. Lokacin da a ka fara cewa an yi hana yin finafinai a Kano kenan a 2001. To, duk wadannan abubuwa su ka fara san a fara tunani.

 

A nan za mu dakata, sai kuma a makon gobe, inda za mu irin gwagwarmayar da ta biyo baya bayan Farfesa Abdalla Uba Adamu ya tsunduma cikin harkar adabi.

A Ko’ina Akwai Zalunci..!

Kalaman mafi yawan mutane a Nijeriya ya fi nuna cewa, an fi aikata zalunci a matakai na gwamnati; kama daga ma’aikatan gwamnati na farar hula, jami’an tsaro zuwa kan masu rike da mukaman siyasa, kamar kansila, shugaban karamar hukuma, ’yan majalisa, sanatoci, gwamnoni da ma kujerar shugaban kasa. To, amma ya wajaba mu sani cewa, a ko’ina a na iya samun zalunci. Kuma duka zalunci, zalunci ne, sannan kuma haramun ne a wajen Allah, kazalika haramun ne a dokokin kowacce kasa, la’alla mutane ne su ka aikata zaluncin a dai-daikunsu ko a kungiyance ko kuma a gwamnatance. Sammakal!

Zalunci ya na iya faruwa a cikin gida tsakanin mata da miji, iyaye da ’ya’ya, uwargida da amarya ko tsakanin masu gida da barori. Duk wanda ya tauye wa wani hakkinsa a tsakan-kanin wadannan mutane masu mabambantan dangantaka, to fa sunan wannan abin zalunci. Idan mace ta ha’inci miji ko ya tauye ma ta hakkinta, zalunci ya faru. Idan iyaye su ka ki sauke hakkinsu a kan ’ya’ya ko ’ya’ya su ka ki yin biyayya da kyautata wa iyaye, zalunci ya wanzu. Idan kishiyoyi su ka kulla sharri a tsakaninsu, zalunci ya tabbata. Haka nan idan masu gida su ka azabtar da barori ko barori su ka aikata almundahana kan masu gida, shi ma zalunci ya afku kenan.

Bugu da kari, zalunci ya na iya faruwa a kamfanoni tsakanin masu kamfani da ma’aikatan kamfanin, tsakanin manyan ma’aikata da kananan ma’aikata ko tsakanin masu binciken kudi daga waje da ma’aikatan kamfanin na cikin gida. Duk lokacin da masu kamfani su ka tauye hakkin gumin ma’aikaci ko shi ma’aikacin ya yi zagon kasa yayin gudanar da aikin da a ka dora ma sa, to zalunci ya faru kenan. Idan manyan ma’aikata su ka shiga hana wa kananan ma’aikata damarsu ko kananan ma’aikata su ka nuna bijirewa umarnin na gaba, to an aikata zalunci. Duk san da masu binciken kudi su ka aikata cin hanci da rashawa ko ma’aikatan cikin gida su ka tafka ha’inci da rufa-rufa, to zalunci ya wanzu kenan a nan.

A matakai na aikin gwamnati kuma zalunci na iya afkuwa tsakanin ma’akata da sauran al’umma. Duk lokacin da wani ma’aikacin gwamnati ya saka ha’inci da almundahana a cikin aikinsa ko al’umma ta dakile ma’aikaci har ya gaza cimma aikata aikinsa, to an aikata zalunci kenan.

Yayin da jami’an tsaro su ka halasta cin hanci da rashawa ko su ka fifita rashawa a yayin gudanar da ayyukansu ko kuma mutanen gari su ka goyi da bayan kama-karya ko amfani da kusanci ba bisa ka’ida ba, to fa babu shakka an tafka zalunci a nan kenan.

Idan masu rike da mukaman su ka siyasa su ka yaudari al’umma ko su ka aikata cin amana ko su ka yi nade-nade bisa son zuciya ko kuma mabiya su ka goyi da bayansu ko masu zabe su ka zabe su ba bisa cancanta ko kuma masoya su ka goya wa masu rike da mukaman siyasa baya a kan son rai, to zalunci ya wanzu kenan.

Ba komai wadannan misalai ke nufi ba face nuni da cewa, a kowane irin mataki ko dangantaka a na iya samun abinda a ke kira da zalunci, ba sai shugabannin da a ka dora wa alhakin tafiyar da ragamar gwamnati ne kawai su ke iya aikata zalunci ba; kowanne a cikinmu zai iya tsintar kansa a inda a ke bukatar ya  kauce wa aikata zalunci, ya kuma guje shi, domin sai kowa ya yi gyara kan damar da ke hannunsa sannan ne gyaran zai kai kowane mataki na kasa da a ke muradin a ga an cimma tun daga ainihin tushen jijiyar tsiron matsalar har zuwa kan ainihin hudar furen.

Tabbas wannan kalubale ne da ke kan kowa! Allah Ya ba mu ikon farkawa yanzu-yanzun nan, don tsamo Najeriya daga sarkakiyar koma-bayan da ta ke ciki. Amin!

Exit mobile version