Hamza Dawaki" />

Sarkakkiya (3)

Portrait of smiling family

08034753238,  hamzadawaki@gmail.com

Ga wanda ya yi katarin bibiyarmu tun daga makonni kusan goma da su ka gabata, na tabbata yana iya fahimtar ashe dai gagarumin aiki ne ibadar da yake yi. Ta zama wuri guda da wani mutum irinsa, amma kuma wanda a kusan komai na rayuwa sun sha bamban! Abu mafi rikitarwa kuma shi ne, kai ba ka san cewa bambancin naku ya kai haka ba. Don haka kana tsammanin ya mu’amalance ka da yadda kake mu’amulantarsa.

Tafiyarmu daga Iyayen Giji na daya har zuwa Mai Gida Kan Gida na hudu, babban burinmu kawai zakulo wasu muhimman muhallai da mu ka sha bamban da juna, musamman a fannin dabi’u. yayin da daga Sarkakkiya na daya kuma mu ka fara karin bayani game da wuraren da bambancin dabi’un yawanci yakan bayuwa ga haddasa rigima a cikin gidajenmu. Wanda ba mamaki wannan ya zama cikamakin wannan gabar. Ba kuma wai don abubuwan ambata a fannin sun tike ba. Sai don watakila zai fi kyau a ce muna tafe muna tattaba bangarorin da dama, domin abin ya fi amfanar mutane da dama. Alabasshi idan hali ya yi wani lokaci mu kara waiwayar gabban.

A wannan karo ma akwai abin da ya kamata a ce mu dan duba a gurguje kafin yi wa batun fitar shantun kadangare kamar haka:

 

Maza Su Kan Shiga Kogo, Mata Kuma Su Yawaita Magana.

Wani muhimmin fanni kuma da maza da mata suka sha bambam a cikinsa, shi ne yadda sukan fuskanci yanayin bacin-rai, ko tashin hankali. Yayin da shi namiji yake samun sauki idan ya warware matsalarsa, ita kuma mace tana samun sauki ne idan ta tattauna game da matsalarta. Idan ba mu san yadda abokan zamanmu ke tunkarar matsalolinsu ba, babu abin da zai hana rikici ya ywaita a tsakaninmu.

 

Misali:

Murja da Isma’il kowannensu ya dawo gida cikin damuwa, saboda matsalarsa da ya ci karo da ita a waje. Isma’il ya zauna yana karatun jarida, cikin tsammanin ko Allah zai sa ya manta da radadin matsalarsa. Ita kuma Murja ta zo ta zauna tana ba shi labarin tata matsalar, da nufin ko idan suka tattauna za ta sami saukin nata radadin damuwar.

Don haka, sai Isma’il ya fara jin haushi, cewa Murja ta cika surutu. Domin shi babu abin da yake bukata a lokacin kamar yin shiru. Yayin da ita kuma Murja wadda babbar buktarta a tattauna matsalarta, ita ma ta fusata, tana jin haushin an ki a kula ta, ba a damu da matsala ko damuwar da take ciki ba!

Irin wannan matsala abu ne da yake faruwa acikin kusan kowanne gida. Kuma warware irin wannan matsalar, ba wai yana da dangantaka ne da karfin son da ma’aurata suke yi wa junansu ba. Yana da dangantaka ne kawai da yadda suka fahimci bambancin dake tsakanin maza da mata.

Idan har Isma’il bai fahimci cewa, mata suna yin magana ne don samun sauki daga irin tasu matsalar ba. Har abada abin da kawai zai yi ta tunani shi ne, Murja ta cika surutu. Don haka yayin da yake son samun nutsuwa sai ma ya ki shigowa gidan, ya sami wani wurin shakatawa mai karancin hayaniya ya yi zamansa. Watakila sai ta yi barci ya dawo gidan. Kamar haka ne kuma idan ita ma ba ta fahimci cewa maza suna bukatar su yi shiru yayin da suke cikin matsala ba, za ta dauka kawai cewa Isma’il ba ya son magana da ita. Don haka ita ma sai ta ci gaba da ‘yan kumbure-kumburenta duk lokacin da ya shigo gidan. Wannan yana daya daga abubuwan da suke sa wasu matan marasa hakuri samun wani dan’uwa ko aboki a waje, wanda za su rika tattauna matsalarsu da shi, da nufin samun wanda zai saurare su, su ji saukin damuwarsu. Wanda kuma hakan zai iya zama bude hanyar kowace irin barna.

 

Yanayin Da Mata Su Kan Tsinci Kansu

 

Yayin Da Mazansu Su Ka Shiga Kogo

Yayin da namiji yake cikin tsananin damuwa, bai isa ya iya samun damar ba wa matarsa cikakkiyar kulawar da take bukata ba. Mata sukan tsinci kansu cikin wani mawuyacin hali a irin wannan lokacin. Domin sau da dama, shi ba ma zai fada mata halin da yake ciki ba, balle ta san cewa yana cikin wani yanayi da ba zai sami damar ba ta waccan kulawar ba. Amma yayin da ya zo ya yi shiru kawai, za ta iya yarda cewa lallai watakila yana cikin damuwa, amma kuma duk da haka ba za ta dena zargi ko jin haushin cewa ya ki kula ta ba. Idan ba ai sa’a ba sai ka ji ita ma ta kufula: “Mutum kawai sai ya je an bato mar rai a can waje ya zo gina ya ishi mutane da kumbure-kumbure!”

A mafi yawan lokaci, mata ba sa fahimtar yanayin da maza sukan kasance yayin da suke cikin damuwa. Tsammaninsu shi ne, namiji ya zauna ya bayyana musu dukkan matsalolin da yake ciki, kamar yadda sukan yi. Yayin da ya ki yin hakan kuma sai ya zama abin zargi, cewa “Idan ba ka gaya min matsalarka ba kuwa wa za ka gaya wa?” Tsammaninta shi ma yana da wani amini da yake zuwa su tattauna abin da ya dame shi da shi, kamar yadda ita ma take da kawar da suke tattauna tata. Amma shi a wurinsa ya fita waje ya yi wani abin da zai dauke mar hankali ya fi mar wannan tattaunawar.

 

Yanayin Da Maza Sukan Tsinci Kansu

Yayin Da Mata Su Ke Magana

Yayin da mace ta shiga cikin yanayin damuwa ta fara magana don ganin ta sami saukin abin da ke damun ta. Shi kuma mijinta sai ya fara damuwa, yana ganin ai wannan korafe-korafen da take yi, ba komai ba ne face kokarin jingina dukkan wani laifin shiga damuwarta a kansa. Bai san cewa tana yin maganganun ne da nufin ta sami saukin matsalolin dake addabar ta ba. Bai fahimci cewa da zai yi shiru ya nuna ya fahimci abin da take nufi ba, ko da bai bude ba ki ya ce ta yi hakuri ba, da sai ta sauko.

Maza suna yin korafi ne kawai saboda abubuwa guda biyu. Ko dai kokarin bayyanar da laifi ga wani, ko kuma neman shawara. Shi ya sa duk lokacin da mace ta yi korafi sai su zata dayan biyun ne. Idan mace ta yi magananu cikin fushi yayin da take bayyana matsalolinta, sai mijinta ya zaci ta na kokarin dora masa laifi ne. Idan kuma ta yi maganar a sannu, cikin nutsuwa, sai ya dauka neman shawara take yi.

 

Idan Namiji Ya Ki Yin Magana

Wani abu da ya ke yi wa mata wahalar fahimta shi ne yadda wataran namiji zai yi shiru, su yi ta magana ba tare da ya tanka ba, domin mata ba su san cewa yayin da namiji ya shiga cikin kogo ba ya son jin magana balle kuma shi ya yi. A tunaninsa yin shirun shi ya fi sauki a kan duk wata magana da za ta fito daga bakinsa. Abinda shi kuma bai sani ba, a duniyar mata a na yi wa mutum shiru ne kawai idan ba shi da wani muhimmanci a rayuwarka.

Ko shakka babu dai, sanin yadda dabi’unmu su ke ya na da matukar muhimmani wurin kyautata zamantakewarmu.

 

Exit mobile version