Daga Sabo Ahmad, Abuja
A Sakonsa na ranar Kirsimata ga kabilar Jaba, musamman mazauna Zariya da kewaye, sarkin Jaba, Yohana Kafarma, da ke zaune a unguwar Hayin Danyaro, Samarun Zariya, ya bukaci al’ummar Jaba mazauna Zariya da su ci gaba da zama da mutamem wannan yanki na Zariya lafiya, kamar yadda suka saba tun lokaci mai tsawo da ya wuce.
Sarkin ya ce, akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin al’ummar kasar Zazzau da ‘yan kabilar Jaba mazauna wannan yanki, saboda haka, ya ce, wannan lokaci na Kirsimati, lokaci ne da za a kara karfafa wannan dangantaka ta hanyar kai ziyara ga juna, da kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a kara sanun hadin kai da taimakon juna.
Kafarma ya ce, yanzu lokaci ne wanda za mu hada kai, ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba, yadda za a samu zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Da yake karin haske, kan dangantakar kabilar Jaba da sauran kabilun wannan yanki mazauna Zariya, ya ce, al’ummar Jaba na da kyakkyawar dangantaka ta dukkan kabilun da ke zaune a wannan yanki na Zariya, kuma taimakon junansu a kowane lokaci.