Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Ganin yadda ake samun ƙaruwar cututtuka da matsaloli irin na kiwon lafiya a Jihar Bauchi, Sarkin Alƙaleri Alhaji Abdulkadir Mohammed ya roƙi gwamnatin Jihar Bauchi da kuma hukumar BACATMA me yaƙi da zazzaɓin cizon sauro a Jiha, kan su himmatu wajen dawo da aikin duba gari a yankunan karkara, domin a magance matsalolin kiwon lafiya da ake fama da su a daidai wannan lokaci.
Abdulƙadir Mohammed ya yi wannan kira ne a lokacin da hukumar BACATMA ta ziyarci garin Alƙaleri domin duba yadda ake aiki da gidajen sauro da kuma raba sabbi ga mutanen da ba su da shi. Inda sarkin ya ƙara da cewa a shekarun baya ba su da matsalar sauro a yankin balle a samu shaharar zazzaɓin maleriya, amma ya zuwa wannan lokaci da mutane suka yawaita tona rijiyoyin burtsatse ruwa ya kasance na gudu a cikin lunguna da magudanan ruwa, an samu yawaitar sauro a yankin lamarin da suke gani ya taka muhimmiyar rawa wajen fama da zazzaɓi da ake yi a daidai wannan lokaci.
Don haka Sarkin ya ce dawo da duba gari zai temaka wajen inganta tsabtar muhalli da kuma magance zubar da shara barkate a cikin gidaje ko yin amfani da magewayi ba yadda ya dace ba. Saboda haka ya ke ganin ya kamata wannan aiki na duba gari a ƙara yawan masu yin sa musamman ganin yadda a halin yanzu yara da dama sun kammala karatu a wannan fanni amma ba su da aikin yi. Don haka idan an ɗauke su za su riƙa shiga cikin gidaje suna bayar da shawarwarin da suka dace don ci gaban ingancin lafiyar al’umma.
Hukumar ta BACATMA tuni ta fara wani shirin rangadin ƙananan hukumomi takwas domin duba yadda mutane ke aiki da gidajen sauro da kuma tabbatar da idan an ba mata gidajen sauron suna aiki da shi ko ba sa yi. Don haka a cikin garin na Alƙaleri aka fara da duba gidan Sarki daga nan kuma aka shiga cikin gidaje ana basu sabbin gidajen sauro da kuma yin gwajin zazzaɓin maleriya wa mutane da basu magunguna kyauta domin shawo kan matsalar zazzaɓin da ake fama da shi a halin yanzu.
Malam Mustpha Yunusa na cikin jami’an hukumar ta BACATMA da suka ziyarci garin na Alƙaleri da ‘yan Jarida kuma ya bayyana cewa wannan hukuma ta himmatu wajen ganin ta yi aiki don rage matsalar zazzaɓin maleriya da ake fama da shi a daidai wannan lokaci. Saboda haka ya ƙara da jan hankalin jama’a su gyara muhallin su domin nesanta sauro da zama cikin su. Bayan haka kuma ya roƙi jama’a su ci gaba da zuwa asibiti a kan lokaci a duk lokacin da suka fahimci ba sa jin daɗin jikin su domin sanin abin da ke damun su saboda a samu damar shawo kan matsalar da ta ke addabar lafiyar su a kan lokaci.