Yusuf Shuaibu" />

Sarkin Argungu Ya Yi Kira Na Musamman Ga Masu Jefa Kuri’a

Sarkin Argungu da ke jihar Kebbi, Alhaji Samaila Mera ya yi kira ga masu jefa kuri’a da su zabi ‘yan takarar da suka dace a babban zaben shekarar 2019, domin tabbatar da ci gaban wannan kasa. Basaraken ya yi wannan kira ne ranar Litinin wajen taro wanda kungiyar ci gaban jihar Kebba tare da hadin gwaiwar hukumar zabe da kungiyar matasan masu san ci gaban yankunan karkara da kuma kungiyar matasan Barewa.

“Ina kira a kan ku tabbatar da cewa mutanen da za ku zaba, mutane ne wadanda kuka amince da su sannan wadanda za su iya adalci wajen gudanar da dokiyokinku, ku zabi mutane  masu gaskiya da rukon amana,” in ji shi.      

Sarkin ya umurci masu unguwannin yankin su fadakar da mabiyansu a kan su zabi ‘yar takara masu halin kirki a kowani mukaman siyasa. Mera ya bukaci kungiyar ci gaban jihar Kebbi da hukumar zabe da kuma sauran kungiyoyin masu zaman kansu da su hada kai wajen fadakar da mutanen yanki domin samun shugabanci na gari.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ta ruwaito cewa, mai unguwar Gulma, Alhaji Bashir Gulma shi ya wakilci sarkin a wajen wannan taro.

A bayanin sa, shugaban kungiyar ci gaban jihar Kebbi Farfesa Sahabi Mahuta ya nanata muhimmacin kungiyar na inganta ci gaban al’ummar jihar ta hanyar kyakkyawar shugabanci a kowani bangare. Ya kara da cewa, kungiyar tana kokarin jan hankalin mutane wajen gudanar da kyakkyawan dimokaradiyya a wannan kasa.   

Mataimakin daraktan ilmantar da masu jefa kuri’a na hukumar zabe Adamu Musa ya bayyana wa mahalarta taro cewa, shirin hukumar zabe shi ne ta gudanar da sahihin zabe. Ya kara da cewa, cibiyar duba zaben za ta yi amfani ta duba korafe-korafen abin da ya faru, sannan za ta inganta na’urar tantance masu zabe lokacin gudanar da zaben.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ta ruwaito cewa, taron ya kunshi tambayoyi da kuma amsa daga mahalarta taro kamar su, dokokin zaben, yakin neman zabe, na’urar tantance masu zabe da rikicin zabe da sauran su.    

Exit mobile version