Sarkin Bai Ya Muna Kyakkyawar Tarbiyya Ta Girmama Jama’a, Inji Iyalansa

Daga Ibrahim Muhammad Kano,

Darakta a Bankin Raya Kasashen Afirka “AfDB”, Dakta Abdu Muktar daya daga cikin ‘ya’yan Marigayi Sarkin Bai, Hakimin danbatta Alhaji Muktar Adnan ya bayyana cewa, duk wani rai mamaci ne. Don haka rashin da suka yi na mahaifinsu sai dai hakuri da dangana da kuma godiya ga Allah bisa kyakkyawan rayuwa da ya yi masa da tsawon rai mai albarka.

Daraktan a bankin raya Kasashen African ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai a madadin zuriyar Marigayi Sarkin Bai a garin Danbatta.

Ya ce, sun sami kyakkyawar tarbiyya daga gareshi duk wasu halaye nagari daga gareshi suka koya, kuma baya fada ko tirsasawa a kan dole, a yi kaza sai dai a koya daga abinda yake aikatawa. Don haka suke koyi da dabi’unsa na iya hulda da jama’a da rashin girman kai da jawo kowa a jiki da hada kan al’umma.

Dakta Abdu Muktar ya yi nuni da cewa girmamawa da ake wa Marigayi Sarkin Bai, hakan na faruwa ne saboda ya girmama kan sane, ta jan girman shi, baya shiga duk wani abu da bai shafe shi ba. Shi ne mutumin da ya yi zamani da Sarakunan Kano guda hudu ya zauna da kowa lafiya, yana kula da jama’a Duk ayyuka da ya yi na gwamnati ba a taba cewa ya yi wani abu na ba daidai ba, wannan na daga abubuwa da suka jawo masa kima.

Ya ce, Sarkin Bai ya rasu ya bar ‘ya’ya 32 daga ciki 4 sun rasu, saura 28 da kuma iyaye mata, sannan akwai jikokin da tattaba kunne, wanda a kirge da suka yi a shekarun baya, sun kai sama da 150.

Abdul Muktar ya ce wani zuwa da ya yi daga kasar Kodebuwa a watan Agusta, sun zauna da Marigayin a Danbatta ya rike hannunsa ya yi masa addu’a har suka je Kano tare ganin Likita daga nan suka je gidan sarauta na Danbazau suka zauna ya dada rike hannunsa ya yi masa addu’a, tun daga lokacin jikinsa ke nuna masa watakila wannan haduwar ita ce ta karshe cikin watan Nuwamba ya yi waya daga Kodebuwa aka hadasu ta waya da suke kallon juna, suka yi magana yanata addu’a da umurni a kan hadin kai.

Ya ce, mahaifin nasu Sarkin Ban Kano ya rasu yana da shekara 95. Kuma daga abin da yakamata al’umma su koya daga gareshi, ya hada da kishin kasa, yana daga cikin wadanda suka tsaya kan samawa kasa yanci, kuma yana da rashin girman kai, kowa nasa ne,baya fada da mutane sai ma hada kansu. Tun daga kan iyalinsa da al’ummar Danbatta da dukkan zuriyar Danbazawa da yake jagoranta.

Exit mobile version