Daga Na’ima Abubakar, Kano
Kamar yadda ya zama al’ada a duk shekara, matasa kan shirya wani kwarya-kwaryar Hawa amma na dokin Kara, Matasa a unguwar Fagge na cikin sahun matasan da kan yi irin wannan hawa a duk bayan sallah, idan Mai martaba Sarkin Kano ya kammala hawan Sallah. Su kuma irin wadannan matasa kan shirya nasu hawan domin nishadantar da al’ummar unguwannin su.
Wannan shekara Sarkin Dokin karan da aka fi sani da Sarki Jamilu ya fuskanci fushin hukuma alokacin da suka kammala shirin fita wannan hawa.
Kamar yadda aka saba ana taruwa a Masallacin waje inda anan ne sarkin ke karbar gaisuwar hakimansa, daga nan kuma sai a zagaya cikin unguwar Fagge inda ake gaisawa da jama’a, kuma Sarkin na tsayawa a wurare daban-daban idan jama’a ke yin gaisuwa harma ana yin addu’a. A ranar Asabar data gabata Sarki Jamilu da tawagar hakimansa suka isa harabar Masallachin na Waje, daga nan ne kuma sai jami’an tsaro suka zo suka umarci sarki da ya kwance rawaninsa, Shi kuma Sarki Jamilu ya basu amsa da cewar Sarki baya kwance rawaninsa a titi, sai dai sarkin ya yiwa Jami’an tsaron alkawarin cewa daga na gida suka nufa.
Tun kafi faruwa wannan al’amari rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta bayar da sanarwa hana duk wani taron al’umma wanda bata tabbatar da sahihancinsa ba domin kaucewa tashin tashina, kamar yadda kakakin rundunanr ‘yan Sandan Jihar Kano DSP Magaji Musa Majiyar ya ambata.