Umar Faruk" />

Sarkin Gwandu Ya Bukaci Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da Sababbin Ubannin Kasa

Masarautar Gwandu ta nemi gwamnatin jihar Kebbi da ta bada umurnin karin nada wasu sabbabi sarakunan gargaji guda shida a matsayin ubannin kasa a cikin masarautar ta Gwandu a jihar Kebbi.

Bayanin neman bukatar bada umurnin karin nada sababbin Sarakunan gargaji gudu shidda a masarautar ta Gwandu ya fito ne daga bakin Basaraken na Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar yayi da yake gabatar da jawabinsa a wurin taron bikin nadin wasu sabbabin Sarakunan gargaji gudu biyu da kuma wasu mutun biyu da aka baiwa mukaman sarautun  gargaji a cikin masarautar ta Gwandu a  jiya a Birnin-kebbi.

An gudanar da taron bikin ne a fadar maimartaba Sarkin Gwandu da ake kira Abdullahi fodiyo palace.

Haka kuma mutanen da aka nada Sababbin Sarakunan gargaji a matsayin Ubannin kasa a yankunansu sun hada da Alhaji Abubakar Abubakar Aliero a matsayin Uban kasar Dan-warai da ke a cikin karamar hukumar mulki ta Aliero da  Sa’idu Abdullahi a matsayin Uban kasar Giro dake cikin karamar hukumar mulkin Suru a jihar ta kebbi.

Sauran da aka nada sun ne Alhaji Abubakar Maigandi Dakingari a matsayin Jakadan Gwandu da kuma cif Sunday John a matsayin Sarkin Idoman Gwandu .

Bisa ga hakan ne Sarkin na Gwandu ya nemi Gwamnan jihar ta kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya sanya hannu da kuma bada umurnin karin nada Sababbin Sarakunan gargaji gudu shidda da ke da saura da ba’a nada ba tun mutuwar wadanda ke bisa karagar gadon sarautar a yankunan nasu. Haka kuma basaraken ya kara da cewar ” baya da kyau abar al’ummar hannu sake batare da nada musu shugaba ba”.

Saboda hakan Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya aike sakon nemi gwamnatin jihar kebbi ta bada dama da kuma yin umurni kan karin nada Sababbin Sarakunan gargaji gudu shidda ta hannun shugaban ma’aikata na fadar gidan gwamnatin jihar, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu wanda ya wakilci gwamna jihar a wurin taron bikin nada ubannin kasar na masarautar ta Gwandu a jiya a Birnin-kebbi.

Hakazalika basaraken ya yi kira ga sabbabin ubannin kasar dasu tabbatar da adalci ga jama’ar yankunansu da kuma jadda gaskiya a tsakanin junna su.  Ya kuma janyo hankulan su wurin ganin cewar sun wanzar da zaman lafiya da kuma  tabbatar tsaro a yankunan nasu.

Bugu da kari ya godewa gwamnatin jihar da kuma sauran al’ummar da suka halarci taron bikin nada Sababbin Sarakunan gargajiyar da kuma bada gudunmuwar su na ganin cewar wannan bikin ya samu nasarar kamamala wa .

Daga karshe ya janyo hankalin uwaye kan su tabbatar da tarbiyar ‘ya’yan su da kuma sanya su makarantun boko da na addini a kuma tabbatar karin zaman lafiya a tsakanin junna kamar yadda aka shedi jihar kebbi da wanzar da zaman lafiya.

 

 

 

Exit mobile version