Sarkin Jama’a Ya Yi Kira Ga Al’ummarsa Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankinsu

Mai Martaba Sarkin Jama’a da ke a cikin jihar Kaduna Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu ya yi kira ga alummar dake a Masarautar sa suci gaba da zaman lafiya da kowa kamar yadda aka sansu da hakan, musamman don a kara samun dauwamammen zaman lafiya a yankin.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin masu rike da mukaman gargajiya da suka hada da, Dagattai, Masu Anguwanni da kuma sauran manyan al’ummar da ke yankin a lokacin da suka kai masa ziyarar girmamawa ta Babbar Sallah a Fadarsa, inda Sarkin ya ce, sai da zaman lafiya ne ake samun dukkan wani ci gaba da ake bukata.

Sarkin wanda ya sanar da hakan a cikin sanarwar da zannan Jama’a Alhaji Dankaka mato, ya sanya hannu ya kuma rabawar da manema labarai a Kaduna yaja hankalin al’ummar sa kada su gajiya wajen yada mahimmancin zaman lafiya a tsakanin al’ummar da ke yankin.

Alhaji Muhammadu ya kuma yi kira ga alummar tasa a kan su ci gaba da bai wa Gwamnatin Tarayya da gwamnatin jihar Kaduna goyon bayan da ya dace, musamman don sauke alkawuran da ke a kansu.

Ya yi nuni da cewa, ta hanyar ba su goyon bayan ne za su iya samun damar inganta rayuwar al’ummar da suke jagoranta.

A karshe Alhaji Muhammadu ya kuma roki yan siyasa da su dinga gudanar da siyasa ba tare da gaba ba.

Exit mobile version