Jamil Gulma" />

Sarkin Kabin Argungu Kan Ranar Samun ’Yanci: Nijeriya Za Ta Wanzu A Kasa Daya

Mai martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Samaila Muhammadu Mera, CON, ya ayyana Nijeriya a matsayin kasar da  za ta cigaba da kasancewa tare da dauwama a zaman kasa guda al’umma daya, wacce ba za ta tarwatse ba.

Ya yi wannan bayanin ne a jiya lokacin da ya ke zantawa da wakilin LEADERSHIP A YAU a fadarsa da ke garin Argungu a jihar Kebbi.

Mai martaba Sarkin Kabin Argungu ya ce, duk da kiraye-kiraye da waDansu ’yan tsirarru ke yi na a raba kasa ba zai yi tasiri ba; Nijeriya za ta cigaba da zama a hade, wanda a maimakon fatan a raba ta, ya kamata a so a nemi hadin kan kowane bangaren kasar ya kawo tasa gudunmawa, saboda Allah ya albarkaci kowane yanki da wani abu da bangarorin kasa ba har kasashen waje su na da bukatarsa.

Bayan albarkatun ma’adanai su da kansu mutane kowane ya na da gudunmawar da zai bayar wajen hadin kan kasa da kuma cigaba.

Basaraken ya ayyana wadanda ke fafutukar ganin an raba kasar a matsayin mutanen da ba su san illar wargajewar kasa ba, inda ya bayyana cewa kasancewar kallon Nijeriya cikin manyan kasashe masu arziki ya na da nasaba ne da zamanta dinkewa sanadiyyar bayar da gudunmawar da kowane bangare ne yi, amma da zarar a ka tarwatsa ta karfin tattalin arzikin kowane yanki zai lalace ya yi rauni, wanda shi ne zai bai wa ’yan kaka-gida damar shigowa su shiga wasoson arziki tare da haddasa husuma tsakaninsu.

Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Mera ya yi tsokaci dangane yadda gwamnati ta yi halin ko oho da masarautun gargajiya, inda ce ba wani waje a kundin tsarin mulki inda a ka ambaci wata dama da a ka bai wa sarakunan gargajiya, don bayar da tasu gudunmawar wajen cigaban kasa duk da ya ke su ne su ka fi kusantar talakawa, su ne madogara ta karshe ga talakawa, musamman wajen abinda ya shafi zamantakewa, wanda sau da yawa akwai abubuwan da ke gagarar gwamnati, wadanda su ka hada da abinda ya shafi rigakafi da tsaro da makamantansu har sai ta hada da masarautu, wanda a sanadiyyar saka hannun masarautun gargajiya ne a ka sami nasarar dakile cutar Shan’inna da yanzu haka a kasar nan yau shekaru uku kenan da cutar ta zama tarihi.

Basaraken ya kuma yi addu’ar zama lafiya mai dorewa tare da samun shugabanni masu tsoron Allah da kuma tausaya wa al’umma wadanda ba son kai ne a gabansu ba.

Exit mobile version