Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home RA'AYI

Sarkin Kano: Idan Har Bai Ji Tsoron Shekau Ba, Me Ya Sa Zai Ji Tsoron Buhari?

by Tayo Adelaja
September 17, 2017
in RA'AYI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare da Maje El-Hajeej Hotoro 08038529660, 08038529660

Albarka da daraja gami da martabar da NAIRA ta yi a baya ne ya sani tunowa, da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi. Har zuwa lokacin da na ke rubutun nan ban yi tsammanin Najeriya ta taba yin gwamnan babban bankin kasa da ya mallaki nagarta irin ta mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ba. Har zuwa lokacin da gwamnatin baya ta cire shi daga wannan matsayin darajar Naira ba ta faduwa kasa warwas kamar yadda ta yi a wannan lokacin ba. Yau ga shi mun tsinci kai cikin mummunan yanayin tsadar kaya sakamakon tashin Dala da karyewar darajar Naira. Kuma wani abin mamaki shi ne yadda a matsayinsa na masanin tattalin arzikin kasa da har yanzu a ka gaza gayyatarsa, domin neman shawarar matakin da ya dace a dauka. Duk da haka bai yi kasa a gwiwa lokacin da ya hango tattalin arzikinmu ya dirfafi afkawa kwazazzabon tabarbarewa, ya garzaya wajen masu ruwa da tsaki na tafiyar da harkokin kasar, ya shaida mu su halin da a ke ciki. Ganin an gaza daukar muhimmin matakin da ya dace, ya shiga kafafen yada labarai ya sanarwa duniya halin da za mu tsinci kanmu matukar ba a gyara ba.

Maimakon a saurare shi a ji me ya ke son fada, sai aka kalle shi a matsayin mai katsalandan da shisshigi tare da fara rubuce-rubucen batanci a kan sa. Wani kuma abin mamaki shi ne a lokacin da ya ke wannan kujera da ya rika fito da kura-kuran gwamnatin baya sai a ka rika yabo tare da yi ma sa jinjina a matsayin gwarzon namiji. Idan ka yarda abubuwan da ya fada a gwamnatin baya gaskiya ne, me ya sa don ya fadi gaskiya a wannan karon zai zama akasin haka? Idan har kasashen duniya masana tattalin arzikin kasa za su yaba ma sa a matsayin jajirtacce kuma ma’abocin sanin harkar tattalin arziki me ya sa mu za mu wofintar da karbar shawara daga gare shi? Idan har a baya ya yi abinda ya taimaki farfadowar tattalin arziki da daga darajar Naira me ya sa yanzu zai bayar da shawarar karya tattalin arziki da durkushe darajar Naira?

Duk wanda zai kwatanta ma ka waye Sanusi Lamido Sanusi, za ce mutum ne maras tsoro da shakkar bayyana abinda ya ke ganin gaskiya ne. Shin wadannan halaye ba su mu ka gani tattare da shugaban kasa Muhammadu Buhari mu ka yi muradin ba shi mulkin Najeriya ba? Me ya sa kuma don mai irin makamancin halinsa ya je gare shi, domin ba shi shawara, sai ya zama laifi? Shin mun manta ne a lokacin da ya na rike da mukami mai daraja na gwamnan banki, ya fito ya bayyana yadda ’yan siyasa su ke lankwame kaso mafi rinjaye na arzikin Najeriya ba? Da su ka dira kansa da zagi gami da suka, bai kare kansa ba? Shin ba a lokacin ne ya samar da manyan ayyukan raya kasa ga jihohin Arewa da wani gwamnan bankin Najeriya bai taba kawo ma na ba? Me ya sa yanzu zai bayar da shawarar da za ta cutar da yankin da ya gina a baya?

A lokacin da ya ke gwamnan banki ne marigayi mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero (Allah Ya Jikansa), ya ba shi sarautar Dan Majen Kano ya kuma gayyaci Muhammadu Buhari bikin nadinsa a matsayinsa na babban dan adawar gwamnatin tarayya. Shin ba mu yi la’akari da rashin tsoro da shakkar da ya nuna ba? Ka na cikin gwamnati mai ci kuma rike da babban mukami, amma ka gayyaci babban dan adawar gwamnatin? Idan har bai ji tsoron rasa mukaminsa a wancan lokacin ba, me ya sa yanzu da ba mukami ne da shi a wannan gwamnatin ba zai ji tsoron bayar da shawara mai amfani? Mun manta yadda ya fito karara ya fada wa duniya yadda gwamnatin da ya ke yi wa aiki ta ke yi wa tattalin arzikin kasa rikon sakainar kashi? Me ya sa wannan karon bai ji tsoron rasa mukaminsa?

Shin ba mu amfana da rashin tsoronsa ba a lokacin da idon mu ya rufe mu ke fatan Buhari ya karbi kasa? Me ya sa yanzu da burinmu ya cika mu ke kyamatar ya ba wa Buhari shawara a kan tattalin arziki? Idan har Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi bai ji tsoron fitowa karara ya fadawa Shekau gaskiya ba, me ya sa zai ji tsoron fadawa Buhari gaskiya? Tunda mu ke a Najeriya a fada min wani mai rike da mukami na siyasa ko sarauta da ya taba fuskantar Shekau, idan ba shi ba? Sai kuma mu rika zagin sa, don zai bayar da shawarar da za ta taimaka ma na wajen farfado da tattalin arzikin kasarmu? Ina kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa, lokaci ya yi da za ka gayyaci Muhammadu Sanusi II, domin taimaka ma ka a sha’anin mulkinka, kamar  yadda ya taimaka ma ka a baya. Yanzu ka fi bukatar sa fiye da yadda ya taimaka ma ka a baya.

SendShareTweetShare
Previous Post

An Kalubalanci Manoman Nasarawa Game Da Ilimin Kwamfuta

Next Post

Tsarin Leadership Ya Burge Ni – Dan Malikin Progress Fm

RelatedPosts

Ayyukan Gwamna Inuwa Sun Burge Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo

Ayyukan Gwamna Inuwa Sun Burge Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

Daga Ismaila Uba Misilli daya daga cikin bangarorin kyakkyawan shugabanci...

Jamhuriyya

Lokaci Ya Yi Da Arewa Za Ta Koma Wa Akidun Siyasar Jamhuriya Ta Farko

by Muhammad
3 weeks ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa, Allah Sarki masu iya magana sun...

Tallafi

Kokarin Jihar Katsina Wajen Raba Tallafin Cutar Korona

by Muhammad
2 months ago
0

Daga Ibrahim Musa Kallah, Jihar Katsina na daya daga cikin...

Next Post

Tsarin Leadership Ya Burge Ni - Dan Malikin Progress Fm

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version