Connect with us

LABARAI

Sarkin Kano Mai Murabus Ya Kalubalanci Babban Sufeton ’Yan Sanda

Published

on

Sarkin Kano Mai Murabus, Muhammadu Sanusi II, ya kalubalanci matsayar Babban Sufeton ’Yan Sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, a gaban kotu kan hurumin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja na sauraron karar da ya shigar ta take hakkinsa a matsayinsa na bil adama.

Idan za a tuna, a wata kara da Sanusi II ya shigar ta bakin lauyansa, Lateef Fagbemi (SAN), ya ce, korarsa da kuma tsare shi da a ka yi sun take hakkinsa na ‘yancin zuwa inda ya so da sauransu bayan da Gwamnatin Jihar Kano ta sauke shi a matsayin Sarkin Kano.
Sai dai kuma a martanin da Sufeta Janar na Najeriya din ya mayar, ya bukaci babbar kotun tarayya da ta yi watsi da karar tubabben Sarkin Kano.

A sukarsa ta farko, Sufeta Janar din ya kalubalanci hurumin kotun na sauraron wannan karar.

A ranar 9 ga Maris, 2020, Gwamnatin Jihar Kano ta tube rawanin Sarki Sanusi, sannan jami’an tsaro su ka fitar da shi zuwa Abuja. Daga bisani kuma an mayar da shi garin Awe na Jihar Nasarawa, inda a ka tsare shi a wani gida har zuwa ranar 13 ga Maris, inda daga nan ne ya samu hukuncin gaggawa daga kotu, wacce ta bukaci a sake shi.

A yayin kalubalantar karar, Sufeta Janar ya musanta korafin da Sanusi ya bayar na cewa, an take hakkinsa bayan sauke shi daga kujerar Sarautar Dabo. Ya ce a Kano ne ya kamata ya shigar da karar, ba Abuja ba.

Ya cigaba da cewa, “zargin take hakkin mai shigar da kara bayan sauke ma sa rawani, duk zai iya tasiri ne a babbar kotun Jihar Kano. Sanannen abu ne cewa, komai ya faru ne a cikin jihar Kano, inda mai karar a ka tube ma sa rawani a matsayinsa na Sarki kuma a ka kai shi Abuja, inda a ka karasa da shi zuwa Jihar Nasarawa.
“A bangarenmu, za mu ce shigarsa Abuja kawai wucewa a ka yi, amma a kan hanyar zuwa Jihar Nasarawa ya ke. Abuja ba za ta taba zama inda a ka danne ma sa hakkinsa ba, don babu abinda ya faru.”

IGP ya kara da cewa, tube rawanin, wanda ya kai ga korar basaraken daga jihar, za a iya shari’ar a Babbar Kotun Jiha ne kawai, ba ta tarayya ba, domin shari’a ce wacce ta shafi tsarin sarauta, inda kuma kotunan tarayya ba su da hurumin sauraron shari’a irin wannan.

Amma kuma Sanusi ya ce, ba karar tube rawaninsa ya kai ba; ya kai kara ne kan yadda ta karfi da yaji da a ka fitar da iyalansu daga fadar kuma a ka kore shi daga Kano tare da tsare shi ne, ya ke kara a kai.

Ya musanta cewa, ba a Kano da Nasarawa kadai a ka take hakkinsa ba, ya na mai cewa, lamarin ya hada da har Abuja da a ka fara kawo shi, kafin a wuce da shi zuwa jihar ta Nasarawa.

Mai Shari’a Anwuli Chikere, wanda tun a baya ya bayar da umarni sakar wa Sarki Sanusi II din marar da ta ba shi damar tafiya Legas ya cigaba da zama a can, ya saka ranar 20 ga Oktoba, don sauraron shari’ar.

 
Advertisement

labarai