Connect with us

LABARAI

Sarkin Kano Ne Zai Dauki Nauyin Musabakar Shekara Mai Zuwa, Inji Sarkin Musulmi

Published

on

An bayyana cewa akwai kyakkyawar danganta tsakanin fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi da Bangaren Gwamnatin Jihar Sokoto, wannan bayani ya fito daga bakin mai alfarma Sarkin Musulmi Dakta Sa’ad Abubakar III alokacin rufe Musabakar Alkur’ani karo na bakwai da ya gudana a Sokoto, Musabakar wadda aka gudanar tsakanin fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi da Kungiyar RABIDA wanda aka shiryawa makarantun
Sakandiren ‘yan mata wanda ba na Arabiyya ba a Jihohin Najeriya. Mai Alfarma Sarkin Musulmi Dakta Sa’ad Abubakar ya ci gaba da cewa samar da wannan Musabaka ta mata na cikin aniyarmu na samar da ingantattun iyaye masu cike da ilimi musamman na addini da kuma na zamani, yace baiwa iyaye mata ilimi tamkar koyar da al’umma ne baki daya, domin duk lokacin da uwa ta kasance ta na da ilimi zaka iske ‘ya’yanta cike da kyawawan tarbiyya, saboda haka ya tabbatar da aniyar fadarsa na ci gaba da hidimatawa harkokin alkur’ani da saura fannonin rayuwa na yau da kullum. Haka Sarkin Musulmin ya Umarci Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da ya dauki nauyin musabar shekara mai zuwa.
Gwamnan Jihar Sokoto wanda ya samu wakilcin shugaban Ma’aikatan Jihar Sokoto Dakta Buhari Bello ya jinjinawa fadar mai alfarma Srkin Musulmin bisa wannan kokari na hidimatawa harkokin ci gaban al’umma, Gwamna ya bayyana bukatar al’umma Jihar Sokoto su ci gaba da hakuri da juna tare da tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu.
Da yake tsokaci kan ayyukan alhairin da Gwamnatin Sokoto ke kan yi, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da ci gaba da tallafawa harkokin musabaka, sannan kuma ya bayyana shirin Gwamnatinsa na samar da makarantun rainon daliban addini wanda za’a fara horar dasu
fannonin addini sama da guda 400 a fadin Jihar Sokoto. A karshe Gwamna Aminu Waziri ya taya wadanda suka samu Nasara da cewa wannan wata baiwa ce daga Allah, haka kuma ya bukaci sauran ‘yan takarar da su fara shirin mubakar shekara mai zuwa domin suma su amfana da irin wannan tagomashin.
Zainab Muhammad daga Jihar Adamawa ceta zama Gwazuwar shekara ta wannan Musabaka ta makarantun Sakandiren da bana Arabiyya ba a matakin Izifi 60, wadda Gwamnan Jihar Sokoto ya bata kyautar kujerar makka, sai kuma wasu kyautukan da suka hadar da kudade, baburan hawa, Na’urar sanyaya abinci, atamfu, alkur’anai da saurana kyaututtuka. Haka kuma A’isha Bashari Abba ta zo na daya a matakin izifi 10, A’isha Abubakar ta daya a izifi 20 daga Jihar Katsina da kuma A’isha Ibrahim izifi 40 daga Jihar Ogun.
Mai alfarma Sarkin Musulmi ya dauki nauyin karatun daliban da suka zo na 1,2,3 har zuwa Jami’a, itama mai dakin Gwamnan Jihar Sokoto wadda Dakta Amamu Yusif ta wakilta ta bayar da gudunmawa Babura da tsabar kudin har Naira Miliyon guda, Iyalan Khalifa Isyaka Rabiu sun gabatar da gudunmawar Naira dubu 500 da sauran kyatuttuka mutane daban daban suka bayar a lokacin bikin rufe musabakar.
Cikin manyan bakin da suka halarci Musabakar akwai Sarakunan Argungun, Sarkin Suleja, Sarkin Gwari, Wazirin Kano wanda ya wakilci Sarkin Kano, sai kuma malamai irinsu Malam Ibrahim Khalil, Alhaji Sabiu Bako, Majalisar Mahaddata alkur’ani ta kasa wadda Gwani Bashir Dan Mahiru ya jagoranci tawagar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: