Kungiyar dalibai ta kasar nan tana ci gaba da kafa kwamitin shugabannin gargajiya da dattawar na kasar nan, domin su taimaka wajen kawo karshen rikicin gwamnati tarayya da kungiyar malaman jami’o’i na kasa wato ASUU da kuma kungiyar malaman kwaleji. A cewar shugaban kungiyar NANS, Danielson Akpan, wadanda za su jagoranci kwamitin dai su ne, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi da kuma sarkin Kano Muhammadu Sanusi.
A cikin bayanin na ranar Lahadi, kungiyar daliban ta bayyana cewa, a cikin kwamitin shugabannin gargajiyar wanda za su shiga takanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar ASUU sun hada har da sarkin Onitsha, Nnaemeka Achebe da kuma Olawo na Owo, Dakta Bictor Olateru-Olagbegi.
Shugaban dattawan kwamitin sun hada da Cif Edwin Clark, Alhaji Tanko Yakassai, Aare Afe Babalola, Cif Innocent Chukwuma, Misis Folorunso Alakija, Farfesa Suleiman Bala Mohammed da kuma shugaban jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Farfesa Rukayat Mohammed tsohuwar minister ilimi.
Mashahuran Lauyoyi guda biyu Messrs Femi Falana da kuma Kayode Ajulo, su ma suna cikin kwamitin.
Akpan ya bayyana cewa, kwamitin zai tattauna da kungiyar ASUU da ASUP da kungiyar ma’ikatan ilimi da masu ruwa da tsaki da kuma gwamnatin tarayya, domin su kawo karshen rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a harkar ilimin kasar nan.
Ya ce, “Tarihi ya nuna cewa ilimi yana da inganci a Nijeriya kamar yadda yake a sauran kasashen duniya, inda wasu ‘yan kasashe suke zuwa jami’o’in Nijeriya. Kafin shekarar 1988 lokacin da aka kafa kungiyar malaman jami’o’in wanda ake kira a yanzu da suna yajin aikin ASUU.
“Ba saban abuba ne a Nijeriya cewa yajin aikin kungiyar ASUU ya kawo wa harkar ilimi cikas a wannan kasa, haka kuma sauran kungiyoyin ilimi suna sun bi sawu. Saboda haka, mun fara tattaunawa tare da samun goyan bayan dattawa da shuwagabannin al’umma ta yadda za a ta zauna da kungiyar ASUU, ASUP,COEASU da sauran kungiyoyi da masu ruwa da tsaki tare da gwamnatin tarayya ta yadda za a kawo karshan lamarin yajin aiki a Nijeriya.”