Nasir S Gwangwazo" />

Sarkin Kano Ya Amince Da Nadin Sani Limanci A Sarautar Santurakin Kutumbawa

Mai  Martaba  Sarkin  Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya amince da nadin tsohon Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Dala da ke Jihar Kano, Hon. Sani Haladu Limanci, a matsayin sabon Santurakin Kutumbawa.

Bayanin hakan ya na kunshe ne a cikin takardar da sarkin ya aike wa Mai Unguwar Kutumbawa, Alhaji Mustapha Abubakar Rimin Kira, mai dauke da sa hannun Madakin Shamaki a madadin Galadiman Kano ranar 20 ga Fabrairu, 2020.

A cikin wasikar  Mai Martaba Aminu Bayero ya umarci  Mai  Unguwa Mustapha Rimin Kira da Yusuf mu su fatan alheri tare da kasancewa mutanen kwarai cikin biyayya ga fadar. ya tabbatar da cewa, an cike dukkan wasu ka’idoji na nadin sarauta a karkashin Masarautar Kano,  kamar yin gwajin shan kwayoyi a hukumar yaki da hana sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta kasa.

Baya ga Hon. Limanci, a cikin wadanda sarkin ya amince da nadin nasu, akwai wasu mutum 15 kuma. A karshe Sarki Bayero ya yi Shi dai Hon. Sani Limanci tsohon sakataren rusasshiyar jam’iyyar ANPP tsawon shekara takwas ne, sannan daga bisani ya shugabanci jam’iyyar shekara biyu da rabi,  kafin  jam’iyyar  ta  narke a cikin majar APC, inda ya rike mukaminta na farko a karamar hukumar ta Dala cikin shekara ta 2014.

Baya ga kasancewarsa cikakken dan siyasa, Malam Sani Limanci kuma ya kasance tsohon malamin makaranta ne shi. Ita dai sarautar Kutumbawa a Kano ta samo  asali ne  daga  Gidan Kutumbawa, wato zuri’ar da  su  ka  mulki  Masarautar Kano  kafin  jihadin  Shehu Danfodiyo.

Exit mobile version