Sani Abdullahi Anwar" />

Sarkin Kano Ya Fanso Fursunoni Da Dama Daga Gidajen Yari

A jiya Litinin ne Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi 11, ya ziyarci gidajen Yari guda biyu da ke Kano don fanso wasu daga Fursunonin da ke can kulle. Ko shakka babu, wannan ba shi ne karo na farko da Sarkin ya yi irin wannan hovvasa ba, duk shekara da ma akwai adadin waxanda ke kullen da ya saba ‘yantowa daga gidajen kason.

A wannan karon, Naira Milyan biyar Sarkin ya biya a matsayin kuxaxen tara da kuma bashi da ya biya wa wasu daga cikin waxannan Fursunoni da ke can kulle a Kurkukun Kurmawa da na Goron Dutse.

Da ya ke jawabi a ziyarar da ya kai gidajen Kurkukun, Sarki Sanusi ya yi wa waxannan Fursunoni wa’azi tare da nasiha ta yadda zaman Kurkukun nasu zai zama wata waqi’a ko darasi a gare su. Har ila yau, ya sake jan hankalinsu wajen ganin sun zama mutanen kirki a cikin al’umma baki xaya, sannan zaman Kurkukun ya zamo musu tamkar wani ilmi na gyaran xabi’unsu da sauran halayyar rayuwa.

Haka zalika, Sarkin ya kuma buqace su da su mayar da al’amaransu ga Allah (SWT), su kuma nemi afuwarsa musamman cikin waxannan ‘yan kwanakin da suka rage mana. Kazalika ya kuma gargaxe su da su zama mutanen kirki masu qoqarin aikata ayyukan alheri a duk inda suka samu kawunansu.

Haka nan, su kuma zama masu kyakkyawan hali domin guje wa dukkanin wasu ayyukan masha’a da zai jawo musu fushin Allah, sannan al’ummar gari su qyamace su, daga qarshe kuma su sake komawa gidan jiya, ma’ana wannan wuri da suke qoqarin bari yanzu.

Idan ba a manta ba, tun a makon da ya gabata Mai Martaba Sarkin, ya qudiri niyyar  fanso waxannan Fursunoni bayan kai wata ziyara ta musamman Kurkukun da ya yi, amma sakamakon qurewar lokaci na rashin samun damar tattaunawa tare da tantance waxanda ake bi bashi, yasa dole Sarkin ya xage har zuwa jiya Litinin.

A qarshe, Muqaddashin Shugaban Kurkukun, Aliyu Yahuza ya yi qarin haske, inda ya bayyana ziyarar Sarkin a matsayin wata manuniya da ke tabbatar da cewa, lallai Sarkin ya damu da talakawansa, yana kuma sane da dukkanin irin halin da suke ciki a wannan jiha tasa ta Kano mai albarka.

Exit mobile version