Sarkin Karaye Na Binciken Dagacin butu-butu Bisa Sayar Wa Bakin Fulani Gona

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Sarkin karaye Dakta Ibrahim Abubakar II ya umarci babban dan majalisar Sarki Injiniya Shehu Ahmed da ya binciki Dagacin garin butu-butu bisa korafin da ake yawan yi a kansa na sayar da fili a yankinsa da ke karamar Hukumar Rimin Gado a Jihar Kano.

Sarkin ya bayar da wannan umarni ne biyo bayan rubutaccen korafin da Hakimin Rimin Gado, Maganin Rafin karaye Alhaji Auwalu Ahmad Tukur ya gabatar wa Sarkin.

A cikin wasikar da aka gabatarwa Sarkin ranar Litinin, Hakimin  ya yi korafin cewa,  wannan dagacin ana zarginsa da sayar da gonar al’umma ga wasu fulani matafiya duk da jan kunnensa da akayi kan hadarin dake tattare da yin hakan, wanda Hakimin na Rimin Gado da Shugaban karamar Hukumar Rimin Gado suka nuna masa, amma basaraken ya yi biris da hakan tare da ci gaba aiwatar da wannan haramtaccen ciniki.

Wasikar ta ci gaba da bayyana cewa, an ja kunnen dagacin cewar kar ya bari a ci gaba da ginin Masallacin a yankinsa, amma ya ba da umarnin ci gaba da ginin Masallacin ba tare da cika ka’i’da ba har aka kammala aikin, a karshe hakan ya haifar da rikici a tsakanin al’ummar garin.

A halin yanzu korafin na gaban hukumar ‘yan sanda, ya yinda da shi kuma babban dan Majalisar sarkin Injiniya Shehu Ahmed tuni ya fara binciken lamarin kamar yadda mai martaba sarki ya umarce shi.

A wani labarin kuma, sarkin na karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II  ya nada Malam Mujittaba Usman a matsayin limamin Unguwar Alhazawa da ke garin Kadana a karamar Hukumar Rogo.

Haka kuma a dai a zaman fadar na litinin Sarkin na karaye ya karbi bakuncin Majalisar limaman karamar Hukumar Kabo suka kai masa ziyarar gaisuwar sallah. Kamar yadda jami’in yada labaran masarautar karaye Haruna Gunduwawa ya shaida wa LEADERSHIP A Yau.

Exit mobile version